DUNIYA
2 minti karatu
Amurka ta sa wa Francesca takunkumi kan neman ICC ta ɗauki mataki kan jami'an Amurka da na Isra'ila
Ba za a ci gaba da lamuntar "gangamin Albanese na siyasa da na tattalin arziki kan Amurka da Isra'ila ba", a cewar Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio.
Amurka ta sa wa Francesca takunkumi kan neman ICC ta ɗauki mataki kan jami'an Amurka da na Isra'ila
The sanctions followed a report by Albanese that identified​​​​​​​ corporations allegedly facilitating Israeli occupation on Palestinian lands. / Reuters
9 Yuli 2025

Amurka ta ƙaƙaba wa jami’a ta Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan Haƙƙoƙin Dan’Adam, Francesca Albanese takunkumi, tana ambato “yunƙurinta na neman” Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta ɗauki mataki kan jami'an Amurka da na Isra'ila.

“A yau na ƙaƙaba wa Jami’a ta Musamman ta Majalisar Dinkin Duniya kan Hakkokin Dan’Adam, Francesca Albanese, takunkumi saboda yunƙurinta wanda bai cancanta ba da kuma abin kunya na neman ICC ta ɗauki mataki kan jami'an Amurka da na Isra'ila, da kamfanoni, da shugabanninsu,” in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, a wani rubutu da ya wallafa a X ranar Laraba.

Rubio ya zargi Albanese da gudanar da wani “yaƙin siyasa da tattalin arziki” kan ƙasashen biyu, yana mai cewa irin waɗannan ayyukan “ba za a ci gaba da lamuntar su ba.”

“Za mu ci gaba da tsayawa tare da abokan hulɗarmu wajen kare haƙƙinsu na tsaron kai,” kamar ya ƙara da cewa.

Takunkumin ya biyo bayan wani rahoto da Albanese ta fitar a makon da ya gabata wanda ya bayyana kamfanonin da ke taimakawa wajen mamayar Isra'ila a ƙasar Falasɗinu, ciki har da Microsoft, da Alphabet, da Amazon, da Palantir waɗanda ke samar da kayan aikin soja, da fasahar sa ido, da kuma kayan gine-gine da ke tallafa wa haramtacciyar mamaya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us