Rasha ta ƙaddamar da hare-hare ta sama mafi girma kan Ukraine a cikin dare, in ji wani jami'in Ukraine, wanda hakan wani ɓangare ne na ƙaruwar hare-haren bama-bamai kan Ukraine ɗin waɗanda ke kawar da fatan da ake da shi na tsagaita wuta.
Rasha ta harba jimillar makamai 537 ta sama kan Ukraine, ciki har da jiragen sama marasa matuƙa 477 da kuma makamai masu linzami 60, kamar yadda rundunar sojin sama ta Ukraine ta bayyana.
Daga cikin waɗannan, an harbo guda 249 yayin da guda 226 suka ɓace, mai yiwuwa saboda an katse su ta hanyar amfani da na'urorin rikirkita su.
Yuriy Ihnat, shugaban sashen sadarwa na rundunar sojin sama ta Ukraine, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa wannan hari na daren jiya shi ne "mafi girman hari ta sama" da aka kai kan ƙasar, idan aka yi la’akari da jiragen sama marasa matuka da kuma makamai daban-daban.
Har ila yau, an kai harin ne a yankuna daban-daban na Ukraine, ciki har da yankin yammacin Ukraine, wanda ke nesa da fagen daga da ake fafata yaƙin.
Poland da ƙasashe ƙawayenta sun tashi jiragen sama don tabbatar da tsaron sararin samaniyar Poland, kamar yadda rundunar sojin sama ta Poland ta bayyana.
Gwamnan yankin Kherson, Oleksandr Prokudin, ya ce mutum ɗaya ya rasa ransa a harin jirgin sama mara matuki.
A yankin Cherkasy, mutum shida sun jikkata, ciki har da wani yaro, kamar yadda gwamnan yankin, Ihor Taburets, ya bayyana.