9 Mayu 2025
Isra'ila ta harba tan 100,000 na bama-bamai a Gaza
Hukumomi a Gaza sun ce Isra'ila ta harba bama-bamai tan dubu dari a Gaza tun bayan kaddamar da kisan kiyashi da ta yi watanni goma sha tara da suka gabata, inda ta kashe ko kuma ta salwantar da Falasdinawa sama da dubu sittin da biyu, sannan ta aikata kisan kiyashi kan mutane sama da dubu goma sha biyu.
Isra'ila dai ta shafe sama da iyalai dubu biyu da dari biyu daga rajistar farar hula gaba daya.
Kazalika wannan gangami ya shafi makabartu, inda sojojin Isra'ila suka sace gawarwaki dubu biyu da dari uku daga kaburburan Gaza tare da kafa wasu kaburbura bakwai a cikin asibitoci, wanda ya zuwa yanzu an gano gawarwaki dari biyar da ashirin da tara.