Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby, a ranar Alhamis ya mayar da martani kan haramcin tafiye-tafiye da Amurka ta kakaba wa 'yan kasarsa, inda ya dakatar da bayar da biza ga 'yan kasar ta Amurka.
“Na umarci gwamnati ta yi aiki bisa ƙa’idar maida martani da dakatar da bayar da biza ga 'yan kasar Amurka,” in ji Deby a wani sako da ya wallafa a X.
“Chadi ba ta da jirage da za ta bayar, ko biliyoyin daloli da za ta bayar, amma Chadi tana da mutunci da alfahari.”
Wannan matakin ya zo ne kwana guda bayan Shugaba Donald Trump ya sanar da haramcin shiga Amurka ga 'yan kasashe 12, ciki har da Chadi, yana mai cewa matakin ya zama dole don “kare” ƙasarsa daga “'yan ta'adda na ƙasashen waje.”
‘Babban haɗari’
Sabon haramcin tafiye-tafiye na Amurka zai fara aiki daga ranar 9 ga watan Yuni.
A cewar Fadar White House, sanarwar za ta hana shigar 'yan ƙasashen da suka haɗa da Afghanistan, Chadi, Jamhuriyar Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Myanmar, Somalia, Sudan da Yemen gaba ɗaya.
An gano cewa waɗannan ƙasashen “ba su da ingantaccen tsari na tantancewa da bincike, kuma an tantance su a matsayin masu babban haɗari ga Amurka,” in ji sanarwar.