AFIRKA
3 minti karatu
Burhan ya ayyana birnin Khartoum a matsayin ‘yantacce bayan sake karɓe iko da filin jiragen sama
Shelar Al Burhan ta biyo bayan wata sanarwar daga gwamnatin jihar Khartoum, wadda ta ce Khartoum ta ‘yantu daga rundunar RSF.
Burhan ya ayyana birnin Khartoum a matsayin ‘yantacce bayan sake karɓe iko da filin jiragen sama
Hafsan sojin Sudan Burhan yana ranganin fadar shugaban ƙasa a Khartoum / Reuters
27 Maris 2025

Shugaban Majalisar Ƙoli ta Sudan Abdel Fattah al Burhan ya isa Fadar Shugaban ƘSasar a babban birnin ƙasar inda ya ayyana Khartoum a matsayin “‘yantacciya" bayan an kori dakarun rundunar RSF.

"Ta ƙare … Khartoum ta ‘yantu," in ji al Burhan, wanda shi ne jagoran soji, a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa cikin gomman sojoji, jim kaɗan bayan da rundunar sojin ƙasar ta sake karɓe iko da Khartoum.

Daga farko ranar Laraba, jami’in gwamnatin jihar Khartoum ɗin ya bayyana a shafin Facebook cewa Khartoum ta ‘yantu daga rundunar RSF.

Dawowar Al Burhan shi ne lokaci na farko da jirgi mai sauƙar ungulunsa ya sauƙa a Khartoum tun lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke kusan shekaru biyu da suka wuce.

Rundunar sojin ƙasar ta bayyana ranar Alhamis cewa ta sake karɓe iko da Fadar Shugaban Ƙasar, yayin da rundunar RSF ta ce ba wani abu ba ne, inda take jaddada cewa hakan ba ya nufin an ci su da yaƙi.

RSF 'ba ta ruguje ba'

Shi kuwa Basha Tabiq, wani mai ba da shawara ga kwamandan rundunar RSF, ya yi watsi da ikirarin da ke cewa sojoji sun yi nasara a Khartoum, yana mai jaddada cewa rundunar ta RSF tana nan daram.​​​​​​​

Tabiq ya rubuta a shafinsa na X cewa rundunar RSF ba ta "ruguje "ba kuma "ba za ta taɓa ruguje ba," yana mai ƙarawa da cewa rundunar sojin ƙasar ba ta cim ma wata "nasara" ba a arangamarsu a Khartoum.

Sai dai kuma ya ƙara daga baya cewa "saboda dalilai na dabarun soji, shugannin sun ɗauki matakin sauya wa dakarunmu wuri a Omdurman saboda dalilai na dabaru da aiki."

Bayan rundunar RSF ta karɓe iko da Khartoum, mahukuntan Sudan sun ɗauke babban birnin ƙasar na wucin gadi zuwa birnin Port Sudan da ke kusa da gaɓar Tekun Bahar Ahmar.

A cikin kwanakin nan, sojin ƙasar ta kuma karɓe iko da muhimman gine-ginen gwamnati da na masu zaman kansu a tsakiyar Khartoum da kuma unguwar al-Muqrin.

Ƙarfin ikon rundunar RSF yana raguwa da gaggawa cikin makonnin nan, inda rundunar sojin ƙasar ta sake karɓe iko da wurare a jihohin Khartoum da Al Jazira da White Nile da North Kordofan da  Sennar da kuma Blue Nile .

Rundunar sojin da kuma ta RSF sun kaure da yaƙi tun tsakiyar watan Afrilu a shekarar 2023, lamarin da ya kashe sama da mutum 20,000 tare da raba mutum miliyan 14 da gidajensu, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma hukumomi na cikin gida.

Bincike daga jami’o’in Amurka, sun yi kiyasin cewa waɗanda suka mutun sun kai kimanin mutum 130,000.

Ƙasashen duniya da MDD sun yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin, inda suka yi gargaɗin cewa matsalar jinƙai muni na tafe yayin da miliyoyin mutane ke fuskantar yunwa da mutuwa saboda ƙarancin abinci.

Yaƙin ya bazu zuwa jihohi 13 cikin jihohi 18 na ƙasar of Sudan.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us