Kamfanin samar da motocin yaki na Turkiyya Katmerciler zai sanya hanny kan yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaki samfurin “Eren” 4×4.
Za a sanya hannu kan yarjejeniyar a wajen taron baje-kolin kayan tsaro na IDEF 2025 a Istanbul, in ji wata sanarwa da kamfanin ya fitar.
Katmerciler zai halarci baje-kolin IDEF 2025 da manyan motocinsa masu sulke na Hizir da samfuri na musamman na O-IKA 2 da motar kasa ta UGV - irin ta ta farko a Turkiyya - wadda ake iya sarrafa makan da ke kanta daga nesa.
Motar Hizir na da sulken bayar da kariya daga bama-bamai da nakiya saboda fasaharta ta armor da injinta mai siffar V, da kuma kujerunta da ke zuke makamashi a lokacin da ake zaune a kan su.
Motar na da inni mai karfin dawaki 400 wadda ke yin aiki sosai a fagen daga a yankunan karkara da birane. Tsarin sarrafa makamanta daga nesa na iya harar abubuwa masu motsi.
Hizir na iya daukar ma'aikata tara, yana iya gudun kilomita 120 a cikin sa'a guda, da kuma ikon hawa tuddai da kashi 70 cikin dari.
Haka kuma, fasahohin Katmerciler na farko na UGV, UKAP, fasahar da aka tattara waje guda daga kamfanonin tsaron Turkiyya guda biyu - Katmeciler-Aselsan - sannan na da fasahar sarrafa wa daga nesa ta SARP.
UKAP na da karfin hawa tuddai da kashi 60 cikin 100, karfin gangara wa ta gefe da kashi 40, na iya tsallaka rami mai fadin millimita 900, kuma na iya daukar kaya masu nauyin tan guda.
Tare da kyamarori na thermal da na wayar hannu da maganadisai da ke auna ayyukan, tsarin na da ayyuka da dama: kuma na iya aiki a matsayin abin hawa mai shata iyaka da gudanar da bincike.
Motar na iya zama mai kubutar da mutane tare da sulkenta da ikon kwashe wadanda aka jikkata daga filin daga, daukar kaya masu nauyi, alburusai, da da kayan aiki, da ma jan motocin da suka lalace.
Furkan Katmerci, mataimakin shugaban Katmerciler, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa kamfanin zai kulla sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwa tare da kamfanin Deftech na Malaysia don mallakar Eren 4 × 4 a wajen baje-kolin IDEF 2025 da ke gudana a Istanbul, inda shugabannin kamfanonin biyu za su halarci bikin sanya hannun.