Matar shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira ga shugabannin ƙasashen duniya su samar da zaman lafiya da yin adalci ta hanyar amfani da diflmosiyya da tasirin ilimi, a wani jawabi da ta gabatar a wurin taron diflomasiyya na huɗu na Antalya Diplomacy Forum (ADF2025).
Da take jawabi a wurin taron mai taken “Gina makoma a Duniyar da ke Fama da Rabuwar Kawuna: Tasirin Ilimi”, Emine Erdogan ta bayyana ilimi a matsayin gishirin rayuwa wanda ke ɗinke kowace irin ɓaraka aka samu.
Ta bayyana cewa taken taron wannan shekarar, “Gina makoma a Duniyar da ke Fama da Rabuwar Kawuna,” ya fito da matuƙar buƙatar da ake da ita ta haɗa kai a yayin da duniya ke fuskantar ƙarin ƙalubale.
‘Bai kamata a saka yara a cikin yaƙi da rikice-rikice ba’
Matar shugaban ƙasar Turkiyya ta ce damar samun ilimi wata tafiya ce da ke kai mutum ga ƙololuewar daraja.
“Abin da yake ƙara mana kuzari a wannan tafiya shi ne ƙwarewar da muka samu yayin da muke nemansa. Za mu fuskanci tsaiko idan ba mu samu tsayayyun matakai ba yayin da muke yin wannan tafiya” in ji ta.
“Babban maƙasudin samun ilimi mai inganci shi ne samar da kowane mutum da zai kasance mai albarka.”
Da take bayani game da miliyoyin ƙananan yara da yaƙi ya hana su samun damar gudanar da rayuwa, Emine Erdogan ta bayyana matuƙar takaici cewa ilimi ya zama wani abu da ba a samu a ƙasashen duniya da dama.
“Ina wannan magana ne cike da matuƙar takaici: a duniyar da muka gaza bai wa ‘ya’yanmu damar rayuwa, damar samun ilimi tana can baya.”