Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya karɓi baƙuncin tawagar Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF.
Gidan talabijin na Nijar ya wallafa bidiyon yadda Mista Zeine ya karɓi baƙin a ofishinsa da ke Yamai a ranar Laraba, 11 ga Yunin 2025.
Tawagar ta IMF ta kai ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin Ms, Ha Vu daga sashen tsimi da tanadi na hukumar ta IMF.
Gwamnatin ta Nijar dai ba ta yi ƙarin bayani kan abin da tattaunawar ta ranar Laraba ta ƙunsa ba.
Sai dai a watan Mayun da ya gabata firaministan na Nijar ya tattauna da mataimakin shugaban da ke lura da ɓangaren Afirka na IMF wato Antonio David kan batun makomar tattalin arziƙin Nijar da kuma ƙaddamar da sauye-sauye domin tattara albarkatu domin inganta yadda ake kashe kuɗin ƙasa tare da inganta harkokin ‘yan kasuwa da kuma samun kuɗi.
A shekarar da ta gabata ne dai IMF ɗin ya sanar da sakin kuɗi na rance har dala miliyan 71 ga Jamhuriyar Nijar.
Haka kuma a Nuwambar bara IMF ɗin ya taya Nijar ɗin murna bayan ya yi hasashen cewa tattalin arziƙin ƙasar zai haɓaka nan gaba