‘Yan sandan Isra’ila sun kai samame wasu wurare a birnin Haifa da ke arewacin ƙasar inda ma’aikatan kafafen talabijin na ƙetare, ciki har da ma’aikatan TRT Arabi, suke aiki, kuma suka ƙwace kayayyakin aikinsu.
Matakin ya biyo bayan wani umarnin daga ministan tsaron ƙasa na Isra’ila mai tsatsauran ra’ayi Itamar Ben-Gvir, wanda ya umarci ‘yan sanda da hukumomin leƙen asiri su hana watsa labarai na kafafen talabijin na ƙetare, yana mai iƙirarin cewa suna "barazana ga tsaron ƙasa."
A cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta ce ta ƙaddamar da aikin ne bisa tseguntawa kuma bisa manufar Ben-Gvir na "rashin haƙuri ." Jami’ai sun kai samame wani ɗakin a wani otel a Haifa, inda rahotanni suka ce wasu na nuna kemera ga tashan jirgin ruwa na birnin.
‘Yan sandan sun ƙara da cewa an yi wa ‘yan jaridan da aka ƙwace kayayyakin aikinsu sammaci domin su ba da bayanai.
TRT Arabi da kuma kafar Al-Ghad TV da ke birnin Alƙahira sun tabbatar da cewa an yi bincike a inda ma’aikatansu suke kuma an ƙwace kayayyakin aikinsu.
Daga farko a ranar, Ben-Gvir ya yi kira ga hukumar leƙen aisrin cikin gida na Isra’ila Shin Bet ta ɗauki matakai kan kafafen watsa labarai na ƙetare.
Ministan mai tsattsauran rai’ayi ya ce rundunar sojin ƙasar ta ba da ƙa’idoji na labaran da za a iya watsawa.
Ben-Gvir ya yi iƙirarin cewa kafafen watsa labarai suna watsa hotunan bidiyo na hare-haren rokoki, yana mai bayyana yin hakan a matsayin wani "laifi." Ya ce shi ya bai wa ‘yan sanda umarnin cewa su ɗauki mataki.
Yayin harin ƙasar Iran cikin sanyin safiyar ranar 15 ga wata Yuni, wani roka daki wata matatar mai a Haifa.
Lamarin, wanda kafar Al Jazeera ta ƙasar Ƙatar ta watsa kai tsaye, ya janyo suka daga kafafen watsa labaran Isra’ila. Tuni dai aka dakatar da ayyukan a matatar man saboda lalacewar.