Tawagar kasuwanci ta Turkiyya ta ziyarci Amurka domin tattaunawa kan huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, musamman manufofin kasuwanci na Washington na baya-bayan nan.
Ma'aikatar kasuwanci ta Turkiyya ce ta sanar da ziyarar a ranar Litinin.
Ziyarar wadda aka gudanar a ranar 22 ga watan Mayu ta biyo bayan ganawar da Ministan Kasuwanci na Turkiyya Omer Bolat ya yi ta intanet a watan Afrilu da Sakataren Harkokin Kasuwanci na Amurka Howard Lutnick da wakilin kasuwanci na Amurka Jamieson Greer.
Trump ya rattaba hannu kan wata doka a farkon watan Afrilu wadda ta kakaba harajin daidaito kan kasashe da dama a fadin duniya, yana mai cewa mafi karancin harajin da kasashen za su na biya shi ne kashi 10 cikin 100, inda wasu kamar Canada, da Mexico, China, da kuma kasashen EU za suna biyan farashi mai yawa.
Turkiyya dai ta fada cikin kasashe da za su na biyan kashi 10 cikin 100.
Tawagar karkashin jagorancin mataimakin ministan kasuwanci na Turkiyya Murat Tuzcu ta ziyarci birnin Washington na kasar Amurka domin ganawa da mataimakin wakilin kasuwanci na Amurka Bryant Trick da sauran jami'ai.
Kazalika ma'aikatar ta yi nuni da cewa, taron ya mayar da hankali ne kan koma bayan da duniya ke fuskanta dangane da manufofin cinikayyar da Amurka ta yi a baya-bayan nan da kuma sabbin manufofin da za a iya dauka don ciyar da harkokin cinikayya na gaba a wannan lokaci.
Yayin ziyarar, an tattauna kan karin wasu matakai da za a dauka don ci gaba da samun nasara kan shekaru 10 na huldar cinikayyar Turkiyya da Amurka, don cimma burin da aka sanya a gaba na kasuwancin dalar Amurka biliyan 100, a cewar ma’aikatar.
A mulkin shugaba Donald Trump na baya, a 2019, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Trump sun amince da kara yawan ƙudaden kasuwancin kasashen biyu zuwa dala biliyan 100.
A lokacin adadin ciniki tsakanin kasashen biyu ya kai dala biliyan 32 a shekarar 2024
Dukkan bangarorin biyu sun tabbatar da cewa, ta kowanne bangare akwai damammaki na kasuwanci da kuma zuba jari tsakanin Turkiyya da Amurka, da kuma fannoni kamar sabbin fasahohi, kirkire-kirkire, masana'antu, ƙirkirrariyar basira ta AI, da kuma tsaron yanar gizo, a cewar ma’aikatar.
Kazalika, bangaren tsaro da makamashi wasu muhimman wurare ne da ake samun ci gaba cikin sauri, in ji ma’aikatar."