DUNIYA
2 minti karatu
Shugaban mulkin sojin Myanmar ya sanar da ranar da za a gudanar da zaɓen ƙasar
Janar Min Aung Hlaing a ranar Juma'a ya ce za a gudanar da zaben ko dai a watan Disamba ko kuma idan ta ƙure Janairun 2026, kamar yadda jaridar Global New Light ta Myanmar ta bayyana a ranar Asabar.
Shugaban mulkin sojin Myanmar ya sanar da ranar da za a gudanar da zaɓen ƙasar
Tuni dai sojojin da ke mulkin kasar suka ce zabe ne babbar manufarsu amma suka yi ta ɗaga ranar zaɓen. repeatedly pushed back the date. / AP
8 Maris 2025

Shekaru hudu bayan ƙwace mulki daga hannun zababbiyar gwamnati, shugaban gwamnatin mulkin sojan Myanmar ya bayyana cewa ƙasar za ta gudanar da babban zaɓe cikin watanni 10, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnati suka ruwaito.

Janar Min Aung Hlaing a ranar Juma'a ya ce za a gudanar da zaben ko dai a watan Disamba ko kuma idan ta ƙure Janairun 2026, kamar yadda jaridar Global New Light ta Myanmar ta bayyana a ranar Asabar.

Ya sanar da ranakun ne a wani taron manema labarai yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar Belarus, daya daga cikin kawayen gwamnatin mulkin sojan Myanmar, yana mai cewa tuni jam’iyyun siyasa 53 suka mika sunayensu domin shiga zaben.

Sai dai Min Aung bai sanar da ainihin ranakun zaben ba.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da yakin basasa a Myanmar, inda aka tilasta wa sojoji shiga fagen yaki da masu fafutukar tabbatar da demokuradiyya da kuma 'yan kabilar da ke neman 'yancin cin gashin kai a galibin kasar.

Ƙwace mulki da sojojin suka yi daga hannun Aung San Suu Kyi a Fabrairun 2021 ya gamu da ƙarin adawa, lamarin da ya jawo sojojin suka ƙara kafewa, sassan ƙasar kuma suka ƙara tsunduma cikin rikici.

Tuni dai sojojin da ke mulkin kasar suka ce zabe ne babbar manufarsu amma suka yi ta ɗaga ranar zaɓen.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us