GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka
Netanyahu dai bai tabbatar ko kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa Shugaban Amurka ya hana shirin kashe Ayatollah ba.
Trump ya hana shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin Iran, in ji jami’in Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani shiri na Isra’ila na kashe jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, in ji jami’an Amurka. / Reuters
16 Yuni 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya hana wani shirin Isra’ila na kashe jagoran addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda wani babban jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.

"Mun gano cewa ‘yan Isra’ila suna da shirye-shiryen kai wa jagoran addinin Iran hari. Shugaba Trump bai amince da haka ba kuma mun shaida wa Isra’ila cewa ka da su aiwatar da matakin," in ji jami’in na Amurka ranar Lahadi, inda ya yi magana da neman a ɓoye sunansa.

Tun da farko, Firaminista Benjamin Netanyahu ya kauce wa wata tambaya game da rahotannin da ke cewa Trump ya umarci ƙasarsa ka da ta kashe Khamenei.

"Ba zan ce komai a kan wannan batun ba," kamar yadda ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News.

"Amma zan iya shaida maka cewa... za mu yi abin da muke buƙatar yi, kuma ina tunanin Amurka ta san abin da zai fi dacewa da Amurka," in ji shi.

Kalaman na zuwa ne yayin da Isra’ila da Iran suka yi musayar rokoki ranar Lahadi, inda aka shawarci mutanen gari su nemi mafaka yayin da ake jin ƙarar ababe a saman birnin Ƙudus, kuma rahotanni ke cewa makamai masu linzami na tsaro sun fara aiki a Tehran.

Bayan gomman shekaru na ƙiyayya da kuma yaƙin bayan-fage da suke yi, rikicin na baya bayan nan shi ne na farko da ƙasashen suka yi musayar wuta mai irin wannan tsananin, lamarin da ya sanya fargaba ta barazanar samun wani rikici da zai iya mamaye dukkan Gabas ta Tsakiya.

An fara shi ne ranar Juma’a, a lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da wasu jerin hare-hare da suka kashe manyan kwamandojin da kuma masana kimiyyar nukiliya  tare da far ma sansanin sojoji da tashoshin nukiliya da kuma gidaje a faɗin ƙasar.

Harin da Tel Aviv ta ƙaddamar ba gaira ba dalili ne ya janyo rikicin, lamarin da ya sa Iran ta ƙaddamar da ramuwar gayya kan Isra’ila.

Hare-haren da kuma hare-haren ramuwar gayyar suna ci gaba da wakana tun wancan lokacin.

Netanyahu ya kuma bayyana wa kafar Fox News cewa Isra’ila ta kashe babban jami’in leƙen asirin Iran Mohammad Kazemi, yana mai cewa nan ba daɗewa ba ne ta "kashe babban jami’in leƙen asirin Iran da mataimakinsa a  Tehran" yayin da jiragen yaƙinta suka kai hare-hare babban birnin ƙasar.

Trump ya jaddada cewa Washington, babbar ƙawar Isra’ila, "ba ta da hannu " cikin hare-haren Isra’ila.

Shugaban Amurka ya jaddada wa kafar ABC News ranar Lahadi cewa Amurka “a halin yanzu” ba ta da hannu a matakan soji.

Ya kuma bayyana cewa shi zai “yarda” idan takwaransa na Rasha Vladimir Putin zai kasance mai shiga tsakani domin warware rikicin.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us