Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra'ila yayin rikicin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari'a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin, wacce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito.
A baya, Ma'aikatar Lafiya ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 606, sannan mutane 5,332 da suka jikkata.
Jahangir ya ce hare-haren Isra'ila kan gidan yari na Evin da ke arewa maso yammacin Tehran sun yi sanadin mutuwar mutum 79, ciki har da fursunoni da ma'aikatan gidan yari, da mazauna yankin.
Ya kara da cewa gidan yarin Evin ya zama ba zai iya aiki ba, kuma an kwashe fursunonin, yana mai kiran harin a matsayin 'tauye hakkin ɗan’adam da kuma karya dokokin kasa da kasa.'
Rikici tsakanin Isra'ila da Iran ya barke a ranar 13 ga Yuni, lokacin da Tel Aviv ta kaddamar da hare-haren sama kan sansanonin soja, nukiliya, da fararen hula na Iran.
Amurka ma ta kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Fordow, Natanz, da Isfahan na Iran, wanda ya ƙara tsananta rikicin.
Tehran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka kan Isra'ila, inda suka kashe akalla mutane 29 tare da jikkata fiye da 3,400, kamar yadda Jami'ar Hebrew ta Jerusalem ta bayyana.
Rikicin ya tsaya sakamakon wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta dauki nauyi, wacce ta fara aiki a ranar 24 ga Yuni.