Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutum uku ‘yan ƙasar Indiya da ke aiki a a wani kamfanin siminti, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Indiya ya tabbatar.
An kama mutanen ne a ranar Talata lokacin da "wasu 'yan bindiga ɗauke da makamai suka kai hari a harabar kamfanin" Diamond Cement Factory da ke Kayes, babban birnin yankin yammacin Mali, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba.
Sanarwar ta ce “ƙarfi da yaji ‘yan bindigar suka ɗauke ‘yan Indiyar uku”.
Haka kuma, ma'aikatar ta ƙara da cewa ofishin jakadancin Indiya da ke Bamako na tattaunawa a-kai-a-kai da gwamnatin Mali da kuma iyalan ‘yan Indiyan da aka sace.
Indiya ba ta bayar da ƙarin bayani kan waɗanda suka kai harin ba ko kuma ko tana tuntuɓar su ba. Sai dai ta bayyana cewa "an kai hare-hare da dama kan sansanonin soja da gine-ginen gwamnati a wurare daban-daban a yammaci da tsakiyar Mali a ranar 01 ga Yuli, 2025."
Tun daga shekarar 2012, Mali tana fama da rikicin 'yan tawaye wanda ya fara a arewacin kasar, ya bazu zuwa sauran sassan kasar har ma ya shafi makwabtan kasashe kamar Burkina Faso da Nijar.