Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana matuƙar damuwa game da sabbin sauye-sauyen da gwamnatin Amurka ta yi wa tsarin bizarta, inda yanzu aka taƙaita bizar da ‘yan Nijeriya za su iya nema zuwa biza mai izinin shiga ƙasar sau ɗaya kuma ta tsawon watanni uku kacal.
Wannan sabon tsarin ya rage wa ‘yan Nijeriya damar da suke da ita a baya na samun bizar shiga ƙasar fiye da sau ɗaya kuma tsawon shekara biyar.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa wannan mataki na Amurka ya saɓa wa ka’idojin mutunta juna, adalci da daidaito, wanda a kullum ya kasance ginshiƙin dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
Gwamnatin Nijeriya ta ce wannan sauyi yana nuna rashin adalci ga masu neman biza daga Nijeriya kuma zai kawo cikas ga daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka.
Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan sabuwar matsaya za ta ƙara ɗora nauyi maras amfani kan 'yan Nijeriya — musamman 'yan kasuwa, ɗalibai, iyalai, da masu tafiya yawon buɗe ido saboda tilas matakin zai sa su rika neman sabuwar biza a-kai-a-kai idan suna son tafiya Amurka da kuma ƙarin kashe kuɗi.
Gwamnatin Nijeriyar ta tabbatar da cewa tuni ta fara tattaunawar diflomasiyya da manyan jami’an Amurka don warware wannan matsala.
Duk da waɗannan korafe-korafe, gwamnatin Nijeriya ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da kyakkyawar dangantaka da Amurka tare da ci gaba da gudanar da tattaunawa ta diflomasiyya har sai an cim ma matsaya da za ta gamsar da bangarorin biyu.
Ana sa ran ci gaba da tattaunawar a cikin kwanaki masu zuwa domin samun mafita mai dorewa.
Yadda matakin Amurka ya shafi Ghana
Sabon tsarin bizar na Amurka ya shafi jama’ar ƙasar Ghana inda su ma ya shafi masu zuwa yawon buɗe ido da ‘yan kasuwa da ɗalibai inda a halin yanzu za a rinƙa ba su biza mai izinin shiga sau ɗaya kuma ta wata uku.
Ma’aikatan diflomasiyya kaɗai da wata nau’in biza mai dangantaka da iyalai Amurkar ta bayar da damar tsawaita wa’adinta ga ‘yan ƙasar ta Ghana.
Wannan sauyi zai rage damar ‘yan Ghana na yin tafiye-tafiye sau da yawa ba tare da sake neman biza ba, wanda hakan zai kara musu kudin tafiya da wahala.