AFIRKA
2 minti karatu
Rikicin Sudan ta Kudu: Shugaban Tarayyar Afirka Mahmoud ya aika tawagar shiga tsakani
Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a Sudan ta Kudu a 'yan makonnin nan, lamarin da ya haifar da fargabar ɓarkewar yaƙi, yayin da taƙaddamar da ke ƙara ruruwa tsakanin Shugaba Salva Kiir da Mataimakinsa Riek Machar.
Rikicin Sudan ta Kudu: Shugaban Tarayyar Afirka Mahmoud ya aika tawagar shiga tsakani
Rikicin Sudan ta Kudu: Shugaban Tarayyar Afirka Mahmoud ya aika tawagar shiga tsakani / Mahamoud Youssouf.X
1 Afrilu 2025

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta ce za ta aike da ‘babbar tawaga’ zuwa Sudan ta Kudu domin warware rikicin siyasar ƙasar da ya kunno kai.

Matakin na zuwa ne bayan Shugaban AU Mahmoud Ali Youssouf ya tattauna da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a daidai lokacin da ake ƙara samun tashe-tashen hankula a ƙasar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta AU ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta jaddada goyon bayanta ga gwamnati da al'ummar Sudan ta Kudu, haka kuma shugaban ya jaddada aniyar ƙungiyar ta AU ta samar da tattaunawa da sulhu da kuma zaman lafiya mai ɗorewa.

Kungiyar ta Tarayyar Afirka ta ce tana aiki tare da gamayyar ƙasashen yankin da kuma MDD a ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin na Sudan ta Kudu.

Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula, inda gwamnati ta tsare mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar a gida a Juba babban birnin ƙasar. An kuma kama manyan abokansa a 'yan makonnin nan.

Gwamnati dai na zargin ɓangaren Machar da ƙoƙarin haddasa rikici a ƙasar.

Gargaɗin Majalisar Ɗinkin Duniya

Sai dai magoya bayan Machar sun yi Allah-wadai da matakin da suka ce ‘‘babban cin zarafi ne’’ ga yarjejeniyar zaman lafiyar ƙasar ta shekarar 2018, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka kwashe shekaru 5 ana gwabzawa da kuma ƙarshen rikicin adawa ta shugabanci tsakanin shugaba Salva Kiir da Riek Machar.

A ranar Juma’a, Sakatare-Janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, yarjejeniyar zaman lafiya ta Sudan ta Kudu tana kan hanyar rugujewa, yana mai kira ga shugabannin ƙasar da su ajiye makamansu tare da sanya dukkan al’ummar Sudan ta Kudu a gaba.

"Ka da mu tauna kalamai: Abin da muke gani ya yi kama da yaƙin basasa na shekarar 2013 da 2016, wanda ya kashe mutane 400,000," kamar yadda Guterres ya shaida wa manema labarai.

Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya ce "yana aiki ba dare ba rana don sassauta tashin hankali da ake ciki - inda ya buƙaci dukkan ɓangarorin su haɗa kai da kuma ƙarfafa kare fararen hula," in ji Guterres.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us