DUNIYA
4 minti karatu
An ƙi amincewa da buƙatar Netanyahu ta jinkirta shari'arsa kan rashawa
Firaministan Isra'ila yana fuskantar zargin cin hanci, da zamba, da cin amana wadanda za su iya kai shi kurkuku idan an tabbatar da su.
An ƙi amincewa da buƙatar Netanyahu ta jinkirta shari'arsa kan rashawa
FILE - Israeli PM Benjamin Netanyahu attends his trial where he faces corruption charges at the district court in Tel Aviv, Israel, Dec. 16, 2024. / AP
27 Yuni 2025

Babban Lauyan Isra'ila ya ƙi amincewa da bukatar Firaminista Benjamin Netanyahu na ɗage shari'ar cin hanci da rashawa da ake yi masa zuwa makonni biyu, kamar yadda gidan talabijin na KAN ya ruwaito.

Netanyahu ya roki Kotun Gundumar Urushalima da ta jinkirta shari'arsa, yana mai cewa yana buƙatar mayar da hankali kan wasu al'amura masu muhimmanci bayan hare-haren Isra'ila kan Iran, ciki har da batun dawo da Isra'ilawa da ake tsare da su a Gaza.

Sai dai, a ranar Juma’a, babban lauyan ya ki amincewa da bukatar Netanyahu ta jinkirta zaman shari’ar da ake sa ran za a ci gaba da yi a ranar Litinin.

Mai shari’a Rivka Friedman-Feldman ta ce, “Dalilan da aka bayar a cikin buƙatar ba za su iya zama hujjar ɗage zaman shari’ar zuwa makonni biyu ba.”

Saboda haka, ana sa ran Netanyahu zai bayyana a gaban kotu a ranar Litinin kamar yadda aka tsara.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Ministan Kudi na Isra’ila Bezalel Smotrich ya soki babban lauyan da alƙalan, inda ya rubuta a shafin X cewa: “Ofishin Babban Lauya da alƙalan gwamnatin Netanyahu sun nace kan zama ƙananan mutane, marasa hangen nesa ko fahimtar gaskiyar lamari.”

Ya ƙara da cewa, “Sun yi kama da waɗanda suka ƙuduri aniyar taimaka mana wajen bayyana wa jama’a girman rashawar da ke addabar tsarin shari’a, da kuma gaggawar buƙatar gyara shi.”

Ministan Tsaron Ƙasa Itamar Ben-Gvir ma ya soki matakin kotun, yana mai bayyana shi “matakin da ya yi nisa da gaskiya kuma abin takaici.”

Ministan Sadarwa Shlomo Karhi ya maimaita wannan suka, yana cewa: “Suna rayuwa a duniyarsu ta daban, sun ware kansu… Sun ji kunya!”

Dan majalisar Likud Avichai Buaron ya ce ya kamata kawai Netanyahu ya sanar da kotu da babban lauyan cewa “aikin da yake yi wa ƙasa da muradin ƙasa sun fi muhimmanci fiye da buƙatar karin zaman shari’a guda hudu, kuma ba zai iya halartar zamn kotun ba a makonni biyu masu zuwa.”

A tsawon watanni da dama, sau biyu kawai Netanyahu ya halarci zaman kotun a cikin mako ɗaya domin amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa, amma an dakatar da zaman shari’ar yayin rikicin Isra’ila da Iran da ya fara a ranar 13 ga Yuni kuma ya ɗauki kwanaki 12.

A ranar Alhamis, Netanyahu ya gode wa Shugaban Amurka Donald Trump saboda kiran da ya yi na a soke shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi masa, matakin da ya janyo cece-kuce da rarrabuwar kawuna a Isra’ila.

Masu goyon bayan Netanyahu sun yi maraba da wannan kiran, yayin da ‘yan adawa suka roƙi Trump da kada ya tsoma baki a tsarin shari’ar Isra’ila.

Jagoran ‘yan hamayya na Isra’ila Yair Lapid ya faɗa a wata hira da kafar yanar gizo ta Ynet: “Muna godiya ga Shugaba Trump, amma… shugaban bai kamata ya tsoma baki a shari’ar wata ƙasa mai cin gashin kanta ba.”

Lapid, wanda ke cikin jam’iyyar Yesh Atid mai matsakaicin ra’ayi, ya goyi bayan wata sanarwa da ɗaya daga cikin abokan kawancen Netanyahu, Simcha Rothman na jam’iyyar Religious Zionism mai tsattsauran ra’ayi, ya yi, inda ya buƙaci Trump da kada ya tsoma baki a shari’ar.

“Ba aikin shugaban Amurka ba ne ya tsoma baki a tsarin shari’a a Jamhuriyar Isra’ila ba,” in ji Rothman, wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin shari’a na majalisar dokokin Isra’ila.

Netanyahu na fuskantar tuhume-tuhume na rashawa, da zamba, da cin amanar jama’a wanda idan aka tabbatar, zai iya kai shi gidan yari.

A watan Janairu, Netanyahu ya fara zaman amsa tambayoyi kan Shari’o’in 1000, 2000, da 4000, wadanda ya musanta. Babban lauyan ya gabatar da tuhume-tuhume kan waɗannan shari’o’in a ƙarshen watan Nuwamban 2019.

Shari’ar 1000 ta shafi karɓar kyaututtuka masu tsada daga attajirai da Netanyahu da iyalinsa suka yi don yin wasu alfarma.

Shari’ar 2000 ta shafi zargin tattaunawa da Arnon Mozes, mai wallafa jaridar Yedioth Ahronoth, domin bayar da kyawawan rahotanni a kafafen watsa labarai.

Shari’ar 4000, wadda aka fi ɗauka da muhimmanci, ta shafi yin alfarma ga Shaul Elovitch, tsohon mai mallakar shafin labarai na intanet na Walla da kamfanin sadarwa na Bezeq, a matsayin fansa domin bayar da kyawawan rahotanni a kafafen watsa labarai.

A watan Nuwamba da ya gabata, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama a Gaza.

Haka kuma Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan ƙare dangi a Kotun Duniya saboda yakin da ta yi kan Gaza.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us