DUNIYA
6 minti karatu
Yawon buɗe idon wasu fitattun mata sararin samaniya yayin da takwarorinsu ke cikin matsi a duniya
Wata tawaga ta mata zalla da ta ƙunshi fitattun mutane ba ta yi wa fafutukar ci-gaban mata wata rana ba. Sharholiya ce kawai da kuma nuna halin ko oho ga miliyoyin mata da ke cikin wahalhalu a duniya.
Yawon buɗe idon wasu fitattun mata sararin samaniya yayin da takwarorinsu ke cikin matsi a duniya
It's a grotesque spectacle - an elite joyride masquerading as social progress. / AP
16 Afrilu 2025

Lokacin da wata tawagar mata zalla - da ta haɗa da mashahuran mawaƙa kamar Katy Perry - suka yi tafiyar minti 11 zuwa sararin samaniya sannan suka dawo, an yaba da wannan a matsayin wani babban ci-gaba ga ƙarfafa mata a fannin kimiyya da bincike.

Amma bari mu faɗi gaskiya: wannan ba ci-gaba ba ne, sharholiya ce kawai. Wadansu attajirai ne kawai suka mayar da fannin sama jannati abin wasa a yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar matsaloli masu tsanani.

To su waye suka yi wannan tafiyar da ake kira da “ƙarfafa mata”?

Yawancin wadanda suka yi tafiyar ba ma 'yan sama jannati ba ne, ba masu bincike ba ne, ba kuma ƙwararru ba ne a fannin sararin samaniya.

Mashahuran mutane ne da masu arziki sosai—an zabe su ne saboda suna da mabiya da yawa ba don wata gudunmawa da za su bayar ga kimiyya ba. Wannan tafiyar gaba daya an shirya ta ne don talla kuma aka sanya mata suna ƙarfafa mata.

Ana ba mu labarai kan yadda aka haɗa kofunan barasa a matsayin nasara aka sha a yayain shawagi cikin yankin da babu nauyin maganaɗisu, yayin da a nan doron duniya kuwa, mata ke cikin halin rasa 'yancin magana da na zabi da narayuwa cikin aminci.

Ko a Afghanistan, inda Taliban suka haramta wa mata damar karatu, ko a Amurka, inda ake tsare da masu ra'ayin 'yanci kamar Rumeysa Ozturk ba tare da dalili ba saboda kawai suna goyon bayan Falasdinawa.

Wannan wani abin kunya ne - wani wasan kwaikwayo na masu arziki da ake nuna shi a matsayin ci-gaba na zamantakewa. Suna so mu yi murna, mu nuna an bire mu, kira lamarin “ƙarfafa gwiwa” - amma babu wani abin ƙarfafa gwiwa game da wani abu da aka shirya don jan hankali da talla wanda ke karkatar da hankalinmu daga rashin daidaito da rashin adalci da wahalhalun da ke addabar rayuwarmu a kullum.

Duk wannan yana faruwa ne a lokacin da duniya ke fuskantar matsalar tsadar rayuwa.

A Amurka, kusan rabin Amurkawa suna rayuwa daga albashi zuwa albashi, wato hannu baka hannu ƙwarya.

A fadin Birtaniya da Turai, miliyoyin mutane na fama da rashin iya biyan kudin ɗumama gida da biyan haya da sayen abinci.

Bankin Duniya ya ruwaito cewa sama da mutum miliyan 700 a duniya har yanzu suna rayuwa da kasa da dala 2.15 a rana.

Yayin da masu arziki ke shawagi a sararin samaniya, miliyoyin mutane suna cikin wahala saboda yaƙin basasa da talauci da hijira.

Misali, a Sudan, Majalisar Dinkin Duniya kwanan nan ta ƙaddamar da wani kiran neman taimako na dala biliyan shida don magance abin da ake kira mafi girman rikicin hijira a duniya.

Zuwa yanzu, kasa da kashi 10 cikin 100 na wannan burin aka cimma. Sama da mutum miliyan 25—rabon al'ummar kasar—na bukatar taimakon jinƙai. Yaro ɗaya na mutuwa a kowace awa biyu a sansanonin 'yan gudun hijira.

A Gaza, sama da mata 10,000 sun mutu tun daga watan Oktoba 2023, a cewar alkaluman baya bayan nan daga ma'aikatar lafiya.

Kuma MDD ta ce tun bayan da Isra'ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta, hare-haren sama sun kashe yara 100 a kowace rana. Mata masu juna biyu da jarirai suna fuskantar mafi tsananin wahala daga hare-haren Isra'ila da ke ci gaba.

Rahoton MDD mai shafi 49 daga watan Maris ya bayyana hare-hare kan asibitocin haihuwa da cibiyoyin kiwon lafiya, da asibitin IVF a Gaza, tare da hana shigar da abinci da magani, lamarin da ya “lalata wani bangare na sauƙaƙa haihuwa ga Falasdinawa a Gaza.”

Amma dole ne mu yi mamakin cewa mawaƙa sun tafi yin shawagi a sararin samaniya.

A duniya, bukatun jinƙai suna ƙaruwa. A shekarar 2024, MDD ta nemi dala biliyan 47 don magance rikice-rikice a duniya—kawai don kare rayuwar mutane.

Amma har yanzu, kusan rabin wannan kudin kawai aka tara.

Rage ba da tallafin kuɗaɗe yana nufin mutane a Gaza da Haiti da Yemen da Congo da Afghanistan suna rasa damar samun abinci da magani da kula da raunuka.

A cikin wannan yanayi da ake ciki, kallon masu arziki suna kwaikwayon zama masu bincike yayin da mawaƙa ke murmushi suna daukar hotunan son burga ya fi zama abin kunya fiye da rashin fahimta.

Yayin da wasu ke shawagi a sararin samaniya cikin kayan alfarma, sama da mutum biliyan 4.5—fiye da rabin al’ummar duniya—ba su da damar samun ayyukan kiwon lafiya na asali.

Harka ta masu ƙumbar susa

A halin yanzu, arzikin mashahuran attajiran duniya ya ƙaru da dala tiriliyan biyu a shekarar 2024, sau uku fiye da shekarar bayanta, inda yake ƙaruwa da kusan dala biliyan 5.7 a kowace rana.

Kamfanin Blue Origin bai bayyana adadin kudin da tafiyar ta lashe ba, amma shafinsa na intanet ya ce kudin farko da ake fara biya don nuna sha’awar sayen tikiti kawai ya kai dala 150,000.

Kuma idan tikitin farko da aka sayar don tafiya a jirgin sama jannatin Blue Origin ya zama wata alama, to da akwai yiwuwar sayen kujerar tafiyar na iya kaiwa miliyoyin daloli.

Cinikin da aka yi wanda ya zo da nasara na dala miliyan 28 ya samu ne daga gwanjon da aka yi da aka samu waɗanda suka nuna sha’awa har fiye da 7,600 daga kasashe 159.

Don haka yayin da wahalhalun da ɗan'adam ke sha ke ƙaruwa, wannan sha'awar yawon shaƙatawa a sararin samaniya ta bambanta sosai da bukatun miliyoyin mutane a duniya.

Idan muna son ƙarfafa mata, to kamata ya yi mu tallafa wa asibitocin haihuwa a Gaza da makarantu ga 'yan mata a Sudan.

Kuma wannan ba tababa ba ce kawai. Wannan shi ne gaskiyar magana.

Idan muna son murnar ci-gaba, dole ne mu daina kambama sharholiya da masu arziki suke yi kuma mu fara magance matsalolin gaske da ke addabar mafi yawan mutane a duniya.

Wadannan wasannin sararin samaniya ba don faɗaɗa bincike ake yin su ba —suna nufin karkatar da hankula yayin da rashin daidaito da rashin adalci, da wahala ke ci gaba da lalata rayuka a duniya.

Idan da a ce masu arziki za su hankalta su yi tunani, to wane irin ci-gaba ne muke murnarsa?

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us