Ba yaƙi, yunwa ko cuta ba — kaɗaici ma yana rage tsawon kwanan mutane a duniya ta hanyar yi musu kisan mummumuƙe, inda dubban mutane ke mutuwa kowace shekara saboda rashin samun wanda za su dinga gaya wa matsalolinsu.
A cikin wani sabon rahoto, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa mutum ɗaya cikin shida a duniya na fama da matsalar kadaici, wanda yanzu ake dangantawa da mutuwar fiye da mutane 871,000 kowace shekara, ko kusan mutum 100 a kowace awa.
WHO ta yi gargadin cewa duniya tana cikin matsalar rarrabuwar al'umma mai tsanani wadda ke da mummunan tasiri ga lafiya, tattalin arziki, da zamantakewa.
Abin da aka taɓa ɗauka a matsayin wata matsala ta mutum ɗaya, yanzu ana kallon kadaici a matsayin wata babbar barazana ga lafiyar duniya.
“Kadaici wata babbar matsalar lafiyar jama'a ce da za a iya kwatanta ta da shan taba da mummuna ƙiba,” in ji Dr Vivek Murthy, wani babban jami’i na WHO, kuma tsohon babban likitan fiɗa na Amurka.
A wata hira da jaridar The Guardian, ya bayyana kadaici a matsayin “wata alama da ke nuna rashin wani abu mai muhimmanci ga rayuwa, wato haɗin kai na zamantakewa,” yana kwatanta shi da buƙatar jiki ta cin abinci.
Illar da kaɗaici ke haifarwa
Kadaici, wanda aka bayyana a matsayin damuwar da ke tasowa daga tazarar da ke tsakanin haɗin kai na zamantakewa da mutane ke so da abin da suke da shi, yana da illa ga lafiya kamar shan sigari guda 15 a rana.
Yana ƙara haɗarin samun cututtukan zuciya, bugun zuciya, ciwon sukari na nau'in 2, damuwa, tashin hankali, har ma da raguwar tunani.
Mutanen da suka keɓe kansu daga zamantakewa suna da yuwuwar fuskantar tunanin kashe kansu ko cutar da kansu.
Illolin kadaici ba su tsaya ga lafiya kawai ba.
Matasa da ke bayyana jin kadaici sun fi fuskantar yuwuwar samun maki marar yawa a makaranta ko ma barin karatu.
Manyan da ke fama da kadaici mai tsanani sau da yawa suna fuskantar wahalar samun aiki ko riƙe shi. A matakin ƙasa, rarrabuwar kai na nufin asarar biliyoyin dala a cikin samar da kayayyaki, ƙarin kuɗin kula da lafiya, da kuma raguwar amincewa tsakanin al'umma.
“A wannan zamani da damar haɗuwa da juna ba su da iyaka, mutane da yawa suna jin kansu sun keɓe kuma suna kadaici,” in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na WHO.
“Baya ga tasirin da yake yi ga mutane, iyalai da al'umma, idan ba a magance shi ba, kadaici da rarrabuwar kai za su ci gaba da jawo wa al'umma asarar biliyoyin dala ta fuskar kula da lafiya, ilimi, da aikin yi,” ya ƙara da cewa.
Ba matsalar ƙasashe masu arziki ba ce kawai
Akasin abin da ake tunani, kadaici ba matsala ce ta tsofaffi a ƙasashen masu arziki ba kawai.
A zahiri, mutane a ƙasashe matalauta suna bayar da rahoton samun matsalar kaɗaici da yawa, kamar kashi 24 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 11 cikin 100 a ƙasashen masu arziki.
Kuma a tsakanin matasa a duniya, har zuwa kashi 21 cikin 100 suna bayar da rahoton jin kadaici, inda mafi yawan waɗanda abin ya shafa samari ne da 'yan mata.
Wasu daga cikin rukunin da suka fi rauni da suka haɗa da 'yan gudun hijira, 'yan ci-rani, masu nakasa, da ƙananan ƙabilu—suna fuskantar ƙarin matsaloli wajen samun haɗin kai, ciki har da nuna wariya, talauci, ko rashin samun damar amfani da kayan more rayuwa na jama'a.
“Ko a cikin duniyar da ke haɗe ta hanyar fasaha, matasa da yawa suna jin kansu a keɓe. Yayin da fasaha ke sake tsara rayuwarmu, dole ne mu tabbatar tana ƙarfafa haɗin kai na ɗan’adam—ba rage shi ba,” in ji Chido Mpemba, Co-chair na Kwamitin da kuma mai ba da shawara ga Shugaban Tarayyar Afirka.
Kira don haɗin kai na duniya
A matsayin martani ga wannan matsalar da ke ƙaruwa, WHO tana kira ga ƙasashe su ɗauki shirin matakai guda biyar da suka haɗa da wayar da kan jama'a don sake tsara yadda al'umma ke kallon haɗin kai na ɗan’adam.
Amma mafita ba ta rataya a wuyan gwamnatoci kawai ba.
WHO tana kira ga mataki a kowane mataki: makarantu, ma'aikata, masu tsara birane, masu kula da lafiya, da kuma kowa da kowa cewa suna da rawar da za su taka.
Daga gina filayen shakatawa da ɗakunan karatu zuwa bayar da magani ko kawai ware lokaci don magana da makwabcinka, matakan rage kadaici sau da yawa suna da sauƙi, amma suna da ƙarfi sosai, in ji hukumar lafiya.