AFIRKA
1 minti karatu
Sojojin Sudan suna ci gaba da kutsawa tsakiyar Khartoum
A makonnin baya baya nan, dakarun rundunar sojin Sudan suna samun galaba a kan mayaƙan RSF inda suka ƙwato jihohi da dama daga hannunsu, ciki har da Khartoum
Sojojin Sudan suna ci gaba da kutsawa tsakiyar Khartoum
Mai magana da yawun rundunar sojin Sudan ya ce sun ƙwato wurare da dama ciki har da fadar shugaban ƙasa / Reuters
23 Maris 2025

Rundunar sojojin Sudan ta ce dakarunta sun samu ƙarin tagomashi a yaƙin da suke yi da dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) inda yanzu haka suke ci gaba da kutsawa tsakiyar birnin Khartoum.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Lahadi ta ce dakarunta suna ci gaba da ƙwace yankuna daban-daban da ke tsakiyar Khartoum daga mayaƙan RSF.

Rundunar sojin ta fitar da wani bidiyo da ya nuna dakarunta yayin da suke ƙwace wani babban shagon sayar da kayayyaki mai suna Al-Waha Mall da ke tsakiyar Khartoum.

Kazalika bidiyon ya nuna dakarun da aka tura yankunan Al Baraka Tower da Babban Masallacin Khartoum da Hotel ɗin Araak.

Kawo yanzu rundunar RSF ba ta ce komai game da wannan batu ba.

Ranar Juma’ar da ta gabata, dakarun rundunar sojin Sudan sun ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum, a karon farko tun da suka soma yaƙi da mayaƙan RSF shekaru biyu da suka wuce.

A makonnin baya baya nan, dakarun rundunar sojin Sudan suna samun galaba a kan mayaƙan RSF inda suka ƙwato jihohi da dama daga hannunsu, ciki har da Khartoum, Al-Jazira, White Nile, North Kordofan, Sennar, da Blue Nile.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us