A wani yunkuri na yaki da ayyukan masu hako ma’adinan kasa ba bisa ka’ida ba a Ghana wanda aka fi sani da Galamsey, hukumar ‘yan sandan kasar ta kama mutane 49 tare da lalata sama da injinan hakar ma’adanai 135.
'Yan sanda sun bayyana cewa, aikin kamen na daga cikin wani bangare na kokarin da ake yi na yaki da ayyukan da ke gurbata muhalli da kuma maido da oda a yankunan da ake hakar ma'adinai.
Samamen dai ya biyo bayan haɗin gwiwa da jami'an leken asiri suka gudanar a yankunan da ake fama da matsalar hakar ma'adanai a yankin Yamma, da Ashanti, da kuma Tsakiya da Gabashin kasar ta Ghana.
A cikin wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar a karshen makon da ya gabata, sun bayyana cewa samamen na su ya mayar da hankali a wuraren harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba kamar a Huniso, da Wassa-Dadieso, da Wassa-Gyapa a yankin Yamma; Akrokerri a yankin Ashanti; Dunkwa-On-Offin da Diaso a shiyyar Tsakiya; da yankin Kogin Awin dake Pankese da Akyem Akwadum a yankin Gabas.
Mahukuntan kasar sun ce samamen sun kawo cikas ga ayyukan hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba tare da kama wasu kayan aikin hakar ma'adinai da dama.
A Yankin Yamma kadai, an kama mutane 19 da ake zargi, sannan sama da kuma injunan canfan 135, wani nau'in na'urar busar da ruwa da aka saba amfani da su wajen hakar ma'adinan kogin-an lalata su.
‘Yan sandan sun kuma kwace injinan fanfo ruwa guda 23, da batura motocin tonon kasa guda hudu a yayin samamen.