KIMIYYA DA FASAHA
3 minti karatu
Musk ya ce an kai wa X gagarumin hari ta intanet
Elon Musk ya ce an kai wa shafin X gagarumin hari ta intanet ranar Litinin, inda matsalar ta shafi masu amfani da shafin na sada zumunta.
Musk ya ce an kai wa X gagarumin hari ta intanet
Elon Musk ne ya mallaki kamfanin sada zumunta na X / AFP
10 Maris 2025

Elon Musk ya ce an kai wa X wani babban hari ta intanet a ranar Litinin yayin da matsalar ke addabar masu amfani da dandalin da aka fi sani da Twitter.

"An kai wani gagarumin harin intanet kan X," in ji Musk a cikin wani sako da ya wallafa a dandalin.

A bara Musk ya yi zargin kai wani hari ta intanet a shafin a daidai lokacin da za a yada wata hira da Donald Trump, sai dai bai bayar da wata shaida ba.

Ana ‘bukatar Kudi mai yawa' don kai harin

Shafin ya lura da zanga-zangar adawa da Ayyukan Sashin Kula da Ayyunakan Gwamnati na Amurka (DOGE) wanda Trump ya bai wa Musk, tare da lalata shagunan Tesla, abin da ke nuna cewa harin na intanet na iya zama wani fushi ne ake nuna wa Musk.

Musk shi ne shugaban Tesla, kamfanin motocinsa masu amfani da lantarki.

"Ana bukatar (kudi) mai yawa kafin kai irin wani hari mai girman gaske," in ji wani sako da ya wallafa a kan abin da shafin Jammies ya wallafa.

"Wane ne ke da dukiyar da zai iya ba da irin wannan kuɗin?"

An samu korafin matsala daga sassa daban-daban na duniya

Musk ya kuma ci gaba da cewa irin wannan harin zai bukaci makudan kudade, yana hasashen cewa aikin wata kasa ne ko kuma babbar kungiya.

Matsalar da aka samu a dandalin na sada zumunta na X ta sa dubun dubatar masu amfani da shafin ba su iya shiga shafin ba, a cewar masu sa ido.

An fara bayar da rahoton fuskanatar matsala a X tun safiyar ranar Litinin, inda masu amfani da shafin a Asiya da Turai, da Arewacin Amurka suka ce ba sa iya shigarsa, a cewar shafin intanet na Downdetector.

Yayin da matsalar ta yi kamari kuwa, sama da mutane 40,000 ne suka ba da rahoton kasa shiga dandalin, in ji shafin.

Yawancin rahotannin sun fito ne daga mutanen da ke ƙoƙarin yin amfani da X a kan wayoyin hannu, amma mutanen da ke amfani da adireshin intanet na shafin su ma sun ba da rahoton matsalar samun damar shiga.

"Har yanzu Twitter na ci gaba da samun matsala?" a tambayar da mai amfani da shafin @Lalaslovely ya wallafa a cikin bangare hira na Downdetector.

Bayan Musk ya sayi Twitter akan dala biliyan 44 a ƙarshen 2022, yawancin ma'aikata sun tafi ko kuma an kore su, abin da ya haifar da damuwa game da ko akwai ma'aikata a wurin don kiyaye dandalin daga dukkan wata matsala da kuma daidaita al’amura.

MAJIYA:AFP
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us