GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Khamenei ya jaddada cewa Iran ba za ta 'taɓa miƙa wuya' ba, ya kuma gargaɗi Amurka
"Ya kamata Amurka ta sani cewa duk wani matakin soja tabbas zai haifar da mummunan ta'adi ," in ji Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei.
Khamenei ya jaddada cewa Iran ba za ta 'taɓa miƙa wuya' ba, ya kuma gargaɗi Amurka
Hours after Trump demanded Iran's surrender, supreme leader Ali Khamenei vowed his country would show "no mercy" towards Israel's leadership. / AFP
18 Yuni 2025

Jagoran Addini na Iran, Ali Khamenei, ya bayyana cewa al’ummar ƙasar ba za su taɓa miƙa wuya ba kamar yadda Shugaba Donald Trump ya buƙata, kuma ya gargaɗi Amurka cewa za ta fuskanci “babban ta’adi” idan ta shigar wa ƙawarta yaƙin.

Jawabin na ranar Laraba ya zo ne bayan kwana shida da ɓarkewar yaƙin, inda Trump ya buƙaci Iran ta “miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba” yayin da yake iƙirarin cewa Amurka na da ikon kashe Khamenei, abin da ya ƙara raɗeraɗin yiwuwar shigar Amurka yaƙin.

Rikicin ya fara ne ranar Juma’a, lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da wasu gagaruman hare-hare da bama-bamai, abin da ya sa Iran ta mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

“Wannan al’umma ba za ta taba miƙa wuya ba,” in ji Khamenei a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na ƙasa, inda ya kira buƙatar Trump “abin da ba za a amince da ita ba.”

“Ya kamata Amurka ta sani cewa duk wani matakin shigar soja ba makawa zai haifar da babban ta’adi,” in ji shi.

Khamenei, wanda yake jagoranci tun 1989 kuma shi ne mai yanke hukunci na karshe kan dukkan al’amuran kasa a Iran, ya yi alƙawarin cewa ƙasar za ta nuna “rashin tausayi” ga shugabannin Isra’ila.

Jawabin ya biyo bayan hare-hare da aka kai cikin dare, inda Isra’ila ta lalata gine-gine biyu da ake amfani da su wajen kera kayan shirin haɗa makaman nukiliyar Iran a kusa da Tehran, kamar yadda Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

“Fiye da jiragen yaƙi 50 na sojan saman Isra’ila... sun ƙaddamar da jerin hare-hare a yankin Tehran cikin ‘yan sa’o’in da suka gabata,” in ji sojojin Isra’ila, suna cewa an kai hari kan wuraren ƙera makamai da dama.

‘Mika wuya ba tare da sharadi ba’

Trump ya kara rura wutar raɗeraɗin cewa Amurka za ta shiga yaƙin, lokacin da ya yi gaggawar barin taron G7 a Kanada, inda shugabannin ƙasashen suka yi kira da a rage tashin hankali amma suka goyi bayan “haƙƙin Isra’ila na kare kanta.”

Ya yi ikirarin cewa Amurka na iya kashe Khamenei cikin sauƙi.

“Mun san daidai inda wanda ake kira ‘Jagoran Addini. yake ɓoye’ Kai masa hari abu ne mai sauki, amma yana cikin aminci a can – Ba za mu kashe shi ba (a kalla ba yanzu ba),” Trump ya rubuta a shafinsa na sada zumunta Truth Social.

Trump ya gana da Kwamitinsa na Tsaron Ƙasa don tattauna rikicin. Ba a fitar da wata sanarwa kai tsaye bayan taron na tsawon awa daya da minti 20 ba.

Jami’an Amurka sun jaddada cewa Trump bai yanke shawara kan shiga yaƙin ba tukuna.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us