Ma’aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye.
Wasu takardu na Ma’aikatar Tsaron Amurka sun kare kasafin kudinta na 2026, inda suka ce kudaden na da manufar horarwa, bayar da kayan aiki, da albashin wata-wata ga SDF da Mayakan Sa Kai na Syria da Amurka ke goya wa baya a kudu maso-gabashin Syria, tare da wasu abokan aiki a Iraƙi da Lebanon.
Bayanan sun nuna cewa kayayyakin sun haɗa da ƙananan makamai tare da kayan kula da lafiya a kayan gyara, “kuma dawowar ‘yan ta’addar Daesh na barazana ga tsaron Amurka, jama’ar Iraƙi, Syria, Lebanon da ma jama’ar duniya baki ɗaya.’
YPG reshen PKK ne a Syria, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda.
Kaso mafi tsoka ya tafi ga ‘yan ta’addar PKK/YPG
Daga cikin dala miliyan 130 da aka ware saboda Syria a kasafin kudin Pentagon na 2026, dala miliyan 7.42 za ta tafi ga Mayakan Sa Kai na Syria, inda bayanan suka ce ana sa ran “kara karfinsu” wajen yaki da gyauron ‘yan ta’addar Daesh a Saharar Badiyah.
Amma kuma mafi yawan kudaden zai tafi ne ga ‘yan ta’addar SDF.
Kudaden baya-bayan nan na zuwa ne bayan an ba su dala miliyan 147.9 a 2025 da dala miliyan 156 a 2024 duk da sunan yaki da ‘yan ta’addar Daesh, matakin da Turkiyya ta nuna kin amincewa da shi saboda ana fakewa da hakan ana bai wa ‘yan ta’adda makamai a kan iyakarta.
A Ayyukan ta’addancin da ta ɗauki shekaru 40 tana yi, PKK, kungiyar da Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin ta ta’adda, ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da fararen hula, mata, da yara kanana.
Turkiyya ta ce bai wa ‘yan ta’addar PKK/YPG makamai ko ma da sunan mene ne, taimaka wa ta’addanci ne kai tsaye.