AFIRKA
3 minti karatu
Sulhun da Turkiyya ta yi wa Ethiopia da Somalia 'abu ne mai muhimmanci': Tarayyar Afirka
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da sulhun da aka yi tsakanin Ethiopia da Somalia wanda Turkiyya ta jagoranta a Ankara ranar Laraba.
Sulhun da Turkiyya ta yi wa Ethiopia da Somalia 'abu ne mai muhimmanci': Tarayyar Afirka
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da sulhun da aka yi tsakanin Ethiopia da Somalia wanda Turkiyya ta jagoranta a Ankara ranar Laraba. / TRT Afrika Hausa
12 Disamba 2024

Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi maraba da sulhun da aka yi tsakanin Ethiopia da Somalia wanda Turkiyya ta jagoranta a Ankara ranar Laraba.

Turkiyya ta jagoranci yin sulhu tsakanin ƙasashen biyu da ke maƙwabtaka da juna bayan sun kwashe kusan shekara guda suna tayar da jijiyoyin wuya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda ya karɓi baƙuncin Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed da shugaban ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud ranar Laraba, ya bayyana sulhun a matsayin wanda ke cike da "tarihi."

Ranar Alhamis, Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya bayyana sulhun a matsayin wani mataki "mai matuƙar muhimmanci da nuna dattako."

'A aiwatar da yarjejeniyar ba tare da ɓata lokaci ba'

"Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya yi maraba da sanarwar da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, da Firaministan Jamhuriyar Demukuradiyyar Habasha Abiy Ahmed Ali suka sanya wa hannu a ranar 11 ga Disamba, 2024 a Ankara, a karkashin jagorancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan,"in ji AU a cikin wata sanarwa.

Kungiyar ta AU ta kara da cewa, "Shugaban hukumar na maraba da wannan muhimmin da ke da matukar muhimmanci na shugabannin Somaliya da Habasha."

Kungiyar ta ci gaba da cewa Faki "yana matukar karfafa musu gwiwa wajen aiwatar da matakan da suka dace ba tare da bata lokaci ba."

"Shugaban ya kara da taya Shugaba Tayyip Erdogan murna bisa goyon bayan da ya bai wa bangarorin biyu bisa kudurinsu na warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa, domin cim ma moriyar kasashensu da al'ummominsu."

Yarjejeniyar shiga tashar jiragen ruwa

Dangantaka tsakanin Habasha da Somaliya ta yi tsami ne a watan Janairu bayan da Addis Ababa ta sanya hannu kan yarjejeniyar shiga tashar jiragen ruwa da yankin Somaliya na Somaliland da ya balle.

A cikin yarjejeniyar, Somaliland za ta bai wa Habasha hayar wani fili mai nisan kilomita 20 a gabar tekun Bahar Maliyadomin kafa sansanin sojojin ruwa.

A daya bangaren kuma, an ce kasar Habasha ta yi alkawarin amince wa da kasar Somaliland. Addis Ababa ba ta tabbatar da rahotannin ba.

Mogadishu ta yi watsi da yarjejeniyar, tana mai cewa "keta" ikonta ne daga Addis Ababa.

Sasantawa karkashin jagorancin Turkiyya

A yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin makwaftan kasashen biyu, Turkiyya ta fara kokarin shiga tsakania watan Mayu, wanda a ranar Larabar da ta gabata aka kai ga cim ma nasara kan kasashen Habasha da Somaliya.

A yayin babban taron da shugaba Erdogan ya shirya a Ankara, Firaminista Abiy da Shugaba Hassan Sheikh sun amince da warware sabanin da ke tsakanin kasashensu domin amfanar 'yan kasarsu, da yankin kusurwar Afirka, da ma nahiyar Afirka baki daya.

Shugaba Erdogan ya ce hanyar da Ankara ta bi a "Yanzu tana kan wani muhimmin mataki."

"Yanzu za mu iya shawo kan wasu damuwoyi, kuma za mu iya bude wani sabon shafi tsakanin Somaliya da Habasha bisa tushen hadin gwiwa da zaman lafiya," in ji Shugaba Erdogan a wani taron manema labarai na hadin gwiwa.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us