Sidi Ould Tah ya zama ɗan kasar Mauritaniya na farko da ya zama shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB) inda ake sa ran sabon shugaban zai yi amfani da dukkan ƙwarewarsa ta kasa da kasa domin tunkarar ƙalubalen da cibiyar ke fuskanta.
Masanin tattalin arzikin mai shekaru 60 da haihuwa shi ne na ƙarshe da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara kuma ya gudanar da yakin neman zaɓe inda ya bayyana shekaru 10 da ya yi a matsayin Shugaban Bankin Larabawa na Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka (BADEA).
Ya yi iƙirarin cewa ya canza shi daga cibiya "wadda ba a san ta ba ga hukumomin ƙididdiga" zuwa ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ci gaba a Afirka.
Magoya bayansa na sa ran cewa zai ƙara haɓaka AfDB kamar yadda ya haɓaka BADEA wadda ke da zunzurutun kuɗi dala biliyan 318.