24 Yuni 2025
An kashe fiye da mutum 40, ciki har da yara da ma’aikatan jinya a harin da ka kai wani asibiti a Sudan a ƙarshen mako, in ji shugaban hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO).
Hari na ranar Asabar kan asibitin Al Mujlad ya faru ne a yankin West Kordofan, kusa da inda aka ja daga tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, waɗanda suke yaƙi tun watan Afrilun shekarar 2023.
Babba daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira da a dena kai hare-hare kan ababen more rayuwa, ba tare da cewa ko wane ne ke da alhaƙin yin hakan ba.
Ofishin WHO a Sudan ya ce an kashe ƙananan yara shida da ma’aikatan jinya biyar a harin, yana mai ba da rahoton cewa an lalace wurin sosai.