AFIRKA
3 minti karatu
An samu mace-macen farko da ke da alaƙa da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaɗuwa cikin sauri
An tabbatar da ƙarin mutane 23 sun kamu da cutar a makon jiya, wanda ya kawo adadin waɗanda suka kamu da cutar zuwa 257 tun lokacin da aka fara gano ta a Ghana a watan Yunin 2022.
An samu mace-macen farko da ke da alaƙa da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaɗuwa cikin sauri
An samu mace-mace na farko da ke da alaka da Mpox a Ghana yayin da cutar ke yaduwa cikin sauri / Reuters
29 Yuli 2025

Ghana ta samu mace-mace na farko da ke da alaƙa da cutar Mpox, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar a ranar Lahadi. Hakan na faruwa ne a yayin da ake samun ƙaruwar sabbin cututtuka a ƙasar da ke yankin Yammacin Afirka.

An tabbatar da ƙarin mutane 23 sun kamu da cutar a makon jiya, wanda ya kawo adadin waɗanda suka kamu da cutar zuwa 257 tun lokacin da aka fara gano ta a Ghana a watan Yunin 2022.


Alƙaluman baya bayan nan sun nuna girma da ƙaruwa na mako-mako da aka samu tun bayan ɓarkewar cutar da kuma mace-macen farko da aka samu a ƙasar.

Ministan Kiwon Lafiya na ƙasar Kwabena Mintah Akandoh ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa “ana kan shawo kan lamarin.”

"Matakin farko na taƙaita ɓarkewar cutar shi ne a iya gano ta da wuri da kuma yadda za a kula da masu ɗauke ita” in ji shi.

Mpox, wadda aka fi sani da cutar ƙyandar biri, cuta ce da ke sanya zazzaɓi, da ciwon jiki kuma tana iya kisa.

Ana dai sa ran hukumar gwamnatin Ghana da ke da alhakin kula da lafiyar jama'a za ta karbi alluran rigakafi daga Hukumar Lafiya ta Duniya(WHO) a wannan makon.

"Mun gano yawan mutanenmu da ke cikin haɗari, kuma a shirye muke mu soma ba da rigakafin cutar da zarar sun iso wurinmu," kamar yadda Franklyn Asiedu-Bekoe wani darakta a ma'aikatar ya shaida wa AFP.


Ɓarkewar cutar a Ghana ta yi nuni da yadda hakan ya zama wani babban ƙalubale a faɗin Yammacin Afirka, inda jami'an kiwon lafiya ke ƙoƙarin shawo kan cutar.

An samu rahoton ɓullar cutar a wannan shekara a yankin Saliyo, inda aka samu adadin mutane 3,350 da suka kamu da cutar, ciki har da mutane 16 da suka mutu, daga watan Janairu zuwa ƙarshen watan Mayu na wannan shekara.

Kazalika, an samu rahoton dubban mutane da suka kamu da cutar a wannan shekara a DR Congo, da Uganda da kuma Burundi, a cewar WHO.

Alƙaluman da hukumar kula da lafiya ta Afirka CDC ta fitar a makon jiya gabata sun nuna fiye da mutane 47,000 ne da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 221 a faɗin nahiyar tun daga watan Janairun bara.

Aƙalla an samu 27,000 daga cikin mutanen a wannan shekarar kaɗai.

A watan Yuni ne daraktan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce har yanzu ƙwayar cutar ta kasance mai barazana ga fannin kiwon lafiya a duniya yayin da ake samun ƙaruwar masu kamuwa da ita a Yammacin Afirka.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us