Matatar Mai ta Dangote ta ce ba za ta janye shirinta na fara dakon mai kyauta da sabbin tankoki masu amfani da gas din CNG ba duk da ruɓanya farashin gas din da aka yi kwanan nan.
Wata sanarwa da matatar ta fitar ranar Alhamis ta ce ruɓanya farashin gas din ba zai hana ta fara amfani da tankoki 10,000 domin dakon mai kyauta a fadin Nijeriya ba.
“Da alama NIPCO, wanda ya fi ƙarfi a harkar CNG a Nijeriya tana wannan ne domin yi wa shirinmu na dakon mai da gas ɗin CNG maƙarƙashiya domin ta gaza aiki,” in ji sanarwar.
Kazalika matatar ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan dakon mai ta NUPENG cewa ba za ta lamunci yin zagon ƙasa wa tattalin arziƙi da sunan gwagwarmayar ƙwadago ba.
“Tun da matatar ta fara aiki, ayyukanmu sun ba da gudunmawa wajen samar wa ƙungiyar kuɗin shiga da ma gudnar da ayyukanta,” in ji matatar.
“Duk da cewa muna maraba da tattaunawa mai m’ana, ba za mu lamunci yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa da tilastawa da tursasawa ba domin samun wata biyan buƙata da sunan gwagwarmayar ƙwadago ba,” in ji sanarwar.
Matatar ta ce tana goyon bayan garambawul da ake yi wa tattalin arziƙin Nijeriya kuma tana sa ran ƙungiyoyi masu sanin ya kamata irin su NUPENG za su yi aiki bisa muradun ƙasa a wannan batu.
Matatar ta kuma ƙaryata rahotannin da ke cewa ta hana direbobin da za su ja tankokin dakon man CNG da ta ɗauka shiga ƙungiyoyin ƙwadago tana mai cewa ita ta yarda da ‘yancin ma’aikata na shiga ƙungiyoyin ƙwadago ko kuma ƙin shiga.
“Zarge-zargen danne ƙungiyar ƙwadago ba su da tushe kuma da alama wani ɓangare ne na yi wa ci-gaban kamfanoni masu zaman kansu zagon ƙasa,” in ji matatar.
Ta bayyana cewa shirinta na fara dakon mai kyauta ta yi ta ne domin tallafa wa manufofin samar da makamashi na ƙasar.
Kazalika ta ce Dangote ba shi da niyyar kasancewa shi kaɗai ne yake da matatar mai da ke aiki a ƙasar, inda ya ƙalubalanci sauran masu kuɗi a ƙasar su shigo fannin a dama da su kamar yadda wasu kamfanonin ƙasar suka shiga harkar siminti.