Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta samu Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin Ansaru, wata ƙungiyar ta’addancin da aka haramta, da laifi tare da yi masa ɗaurin shekara 15.
Usman, wanda aka fi sani da suna Abu Barra, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi a gaban kotu, kuma ya amsa laifin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.
Laifukan da suka saɓa wa doka su suka ba shi damar sayen makamai domin ta’addanci da garkuwa da mutane, in ji takardar tuhumar da aka yi masa.
Sai dai alƙalin kotun, Maishari’a Emeka Nwite, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun DSS har zuwa lokacin da za a yi masa shari’a kan sauran tuhume-tuhume 31 da hukumar ta yi masa.
A cikin takardar ƙara mai tuhume-tuhume 32 da DSS ta gabatar a gaban babbar kotun gwamnatin tarayyar, an tuhumi Usman da Abubakar Abba da aikata ayyukan ta’addanci a shekarar 2022 ta hanyar kai hari kan barikin Wawa Cantonment na sojin Nijeriya a Kainji, New Bussa, da ke ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja.
An kuma yi zargin cewa sun samu horo kan amfani da makamai da kuma haɗa bamabamai a sansanonin ‘yan ta’adda.
Kazalika an tuhume su da samun horo kan dabarun yaƙi daga wata ƙungiyar ta’addanci a ƙasar Mali.
Bayan ɗaurin na shekara 15, Mai shari’a Nwite ya saka ranar 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar shari’ar sauran tuhume-tuhume da ake yi masa.
Hukumar DSS ta zargi kwamandodin kan kitsa harin watan Yulin shekarar 2022 a gidan yarin Kuje da ke Abuja inda suka kuɓutar da fursunoni 600.
Kazalika an zarge su da kitsa hari kan tashar yuraniyom ta Jamhuriyar Nijar da kuma garkuwa da mutane ciki har da garkuwa da Injiniya ɗan Faransa Francis Collomp a shekarar 2013.
Baya ga haka, sun kuma aikata wasu laifuka ciki har da garkuwa da Alhaji Musa Umar Uba, Magajin Garin Daura a shekarar 2019 da kuma wasu jeri fashi da makamai.
Ribadu ne ya sanar da kama su
A kwanan baya ne, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya sanar da kama kwamandojin.
Ya bayyana cewa an yi nasarar kama su ne bayan ayyukan haɗaka na jami’an tsaro.
Ribadu ya bayyana Usman a wanda yake ce wa kansa “Amir” na “Ansaru” a matsayin wanda ya jagoranci gungun ‘yan ta’adda a faɗin ƙasar.
Ya ce Mamuda ya yi aiki a matsayin “shugabna ma’aikatansa,” inda ya jagoranci ‘yan ta’addan “Mahmudawa” kusa da gandun dabbobi na ƙasa a Kainji.
Ansaru dai ta bayyana ne a watan Janairun shekarar 2012 inda ta ɓalle daga Boko Haram.