NIJERIYA
3 minti karatu
Likitoci masu neman ƙwarewa sun tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya
Matakin ya biyo bayan cikar wa’adin sa’a 24 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya cewa ta biya bukatunta.
Likitoci masu neman ƙwarewa sun tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya
Likitocin na bukatar a biya su kuɗaɗen Asusun Horarwa na Likitoci na 2025 da suke bi bashi, / Reuters
13 awanni baya

Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa a Nijeriya (NARD) ta tsunduma yajin aiki, inda ta umarci ma’aikatanta da su dakatar da ayyuka a duka asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar daga ranar Jumma’a.

Matakin ya biyo bayan cikar wa’adin sa’a 24 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya cewa ta biya bukatunta.

Jaridar Daily Trust ta ce a safiyar Jumma’a, Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta NARD, Dr. Tope Osundare ya tabbatar mata cewa sun fara yajin aikin.

“Abin takaici, ba a biya mafi karancin bukatunmu ba a cikin wa’adin sa’a 24 da aka ba su, kuma yajin aikin ya fara ne da safiyar yau (Jumma’a) kamar yadda kwamitin gudanarwa na ƙungiyar ya umarta,” in ji shi a cikin wani saƙo.

Tun a ranar 1 ga watan Satumba ne ƙungiyar NARD ta yi gargaɗi cewa za ta tsunduma yajin aiki idan gwamnati ta gaza biyan buƙatunta cikin kwana 10.

Likitoci masu neman ƙwarewar, waɗanda su ne mafi yawa a fannin lafiyar ƙasar a asibitocin koyarwa da na ƙwararru, sun sha tafiya yajin aiki a ‘yan shekarun nan kan rashin biyansu albashi da rashin inganta walwalarsu da kuma rashin kyakkyawan yanayi aiki.

Me likitocin suke buƙata?

Likitocin na bukatar a biya su kuɗaɗen Asusun Horarwa na Likitoci na 2025 da suke bi bashi, da gaggawa, da biyan basussukan watanni biyar daga duban tsarin albashi na kashi 25 zuwa 35 cikin 100, da sauran makudan kudaden albashin da suka dade suna taruwa.

Sauran sun hada da biyan bashin alawus-alawus na 2024, da gaggawar bayar da alawus-alawus na ƙwararru, da maido da amincewa da takardun shaidar zama mamba na Afirka ta Yamma.

Har ila yau, sun yi kira ga Kwalejin Kiwon Lafiya ta Kasa da ta ba wa duk wanda ya cancanta takardar shaidar zama mamba, da aiwatar da tsarin albashin CONMESS na 2024, magance matsalolin walwalar jama’a a Jihar Kaduna, da magance matsalolin da likitocin da ke zaune a asibitin koyarwa na LAUTECH, Ogbomoso.

Osundare ya ce kungiyar ta amince da alkawarin da gwamnati ta yi na magance matsalolinsu amma ta dage cewa dole ne ta ɗauki matakin gaggawa na tafiya yajin aiki.

Ya ce: “Gwamnatin tarayya ta kira mu a jiya (Laraba) kuma ta yi alkawarin magance mana matsalolin da ke damunmu.

“Mun yi taronmu kuma bayan tattaunawa ta tsawon sa’o’i shida, mun yanke shawarar bai wa gwamnati sa’o’i 24 masu zuwa don tabbatar da biyan kudaden MRTF ga wadanda za su amfana, domin MDCN ta inganta takardar shaidar zama mamba ta mu da kuma biyan sauran bukatunmu.

Tun da fari ya ce “Idan babu abin da ya faru kafin karshen yau (Alhamis), za mu fara yajin aiki ba tare da ɓata lokaci ba a gobe (Jumma’a).

Da aka tambaye shi ko yajin aikin gargadi ne, sai ya ce “Za mu yi nazari bayan Gwamnatin Tarayya ta yi abin da ya dace.”

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us