WASANNI
2 minti karatu
Barcelona ta koka kan haramta wa Mbappe buga wasa ɗaya kacal saboda samun jan kati a makon jiya
Barcelona ta soki hukuncin haramta wa ɗan wasan Real Madrid Kylian Mbappe buga wasa guda kacal, sakamakon samun jan katin a wasan Madrid da Alaves.
Barcelona ta koka kan haramta wa Mbappe buga wasa ɗaya kacal saboda samun jan kati a makon jiya
/ Reuters
16 Afrilu 2025

Mataimakin shugaban Barcelona, Rafa Yuste ya soki hukuncin haramcin buga wasa ɗaya da aka bai wa ɗan wasan Real Madrid Kylian Mbappe, sakamakon samun jan kati a wasan Madrid da Alaves.

Yuste ya kira hukuncin da “abin kunya”, saboda ya ci burin a ce an hana Mbappe buga wasa biyu ko fi, wanda zai sa ba zai iya buga wasa na biyu da ke gaban Madrid ba, wanda za su yi da Barca.

Shahararren ɗan wasan gaba na Madrid ya samu jan kati a wasan gasar La Liga da suka doke Alaves da ci 1-0 a ƙarshen makon jiya.

Mbappe ya yi wa ɗan wasan tsakiya na Alaves, Antonio Blanco ƙeta yayin ƙoƙarin ƙwace ƙwallo. Hakan ya sa alƙalin wasa ya sallame kai-tsaye a minti na 38.

Masu nazarin ƙwallo da dama sun yi tsammanin za a hukunta Mbappe da haramcin wasa sama da ɗaya, amma sai kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon Sifaniya ya yanke hukuncin hana masa wasa guda kawai.

Wasan ƙarshe

Kylian Mbappe zai ƙauracewa wasan Real Madrid mai zuwa tare da Athletic Club. Sai dai zai iya buga wasan gaba wanda wasan ƙarshe ne na gasar Copa del Rey tare da Barcelona.

A ra’ayin mataimakin shugaban na Barcelona, girman hukuncin bai kai munin muguntar da Mbappe ya yi ba.

Shafin Goal ya ambato Yuste yana faɗawa ‘yan rahoto cewa, “[Laifin na Mbappe] da kuma hukuncin abin takaici ne. Mummunan laifi ne da zai iya jikkata abokin wasansa."

A bana Barcelona da Real Madrid sun haɗu sau biyu a gasar La Liga da ta Spanish Super Cup, kuma Barca ta yi nasara a duka wasannin biyu.

Kafin ƙarshen kakar bana, Barca da Madrid za su sake karawa sau biyu, a gasar La Liga da kuma wasan ƙarshe na Copa del Rey ranar 26 ga watan nan na Afrilu.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us