AFIRKA
2 minti karatu
SONIDEP ya bayar da tabbacin ɗaukar matakan magance matsalar ƙarancin fetur a Nijar
A wani jawabi da ya yi a gidan talbijin na Nijar, daraktan kasuwancin kamfanin SONIDEP, ya ce cire tallafin mai da aka yi a Nijeriya ya sa mai ya yi tsada a ƙasar mai maƙwabtaka da Nijar lamarin da ya hana shigowa da mai Nijar ta ɓarauniyar hanya.
SONIDEP ya bayar da tabbacin ɗaukar matakan magance matsalar ƙarancin fetur a Nijar
Yanzu ƙasar Nijar ta dogara ne da man da ake samarwa a hukumance, maamakon man 'yan bunburutu / Getty Images
10 Maris 2025

Yayin da ake fama da ƙarancin man fetur a babban birnin Nijar, Yamai, kamfanin man ƙasar (SONIDEP) ya yi bayani dangane da silar  ƙarancin fetur tare da ba da tabbacin cewa yana aiki domin magance matsalar.

A wani bayani da ya yi a gidan talabijin na ƙasar, daraktan kasuwanci da cinikayya na kamfanin SONIDEP, Maazou Oumani Aboubacar, ya ce cire tallafin mai da aka yi a Nijeriya ya sa mai ya yi tsada a ƙasar mai maƙwabtaka da Nijar lamarin da ya hana shigowa da mai Nijar ta ɓarauniyar hanya.

Ya ƙara da cewa ƙoƙarin dakarun tsaron ƙasar kuma ya hana cuwa-cuwa a harkar man fetur wadda a baya ta kai kimanin kashi 40 zuwa 50 cikin 100 na man fetur ɗin da ake amfani da shi a ƙasar.

  Aboubacar  ya ce a yanzu ƙasar ta fi dogara ne kan man da ake tacewa daga matatar man ƙasar (SORAZ) wadda a halin yanzu ke samar da tankar mai 25 na man fetur a yini.

"Muna samun tankar mai 25 ne a kowace rana, yayin da buƙatar babban birnin ƙasar kawai ta kai tankar mai 25 zuwa 26, kuma buƙatar ƙasar gaba ɗaya ta kai tankar mai 40 zuwa 50," in ji daraktan.

Maazou Oumani ya tabbatar wa ‘yan Nijar cewa ƙasar na da mai da yawa a birnin Lomé na ƙasar Togo.


 "Tankokin man na kan hanyar su domin tabbatar da samuwar mai ga ƙasar," in ji shi yana mai ƙarawa da cewa "SONIDEP na da mai a ƙetare wanda muke ƙoƙarin ɗaukowa ta ko wace hanya."


Wannan bayanin na zuwa ne dai a daidai lokacin da ake fama da ƙarancin mai a ƙasar ta Nijar inda masu ababen hawa ke layi domin samun man fetur.


Kuma ‘yan Nijar suna fatan cewa tanokin man fetur ɗin da aka yi shelar kawowa za su zo ba da jimawa ba domin magance matsalar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us