Saɓanin labaran da ake yayatawa a shafukan sada zumunta, tsarin da Nijeriya ke bi wajen sayar da ɗanyen mai ga matatun man da ke ƙasar na aiki har yanzu, in ji gwamnatin ƙasar.
Wata sanarwar da shugaban wani kwamitin ƙwararru cikin tsarin kuma shugaban hukumar tattara harajin tarayyar Nijeriya, Zach Adedeji, ya fitar ta ce ba a hana matatun man ƙasar sayen ɗanyen mai ba.
“Waɗannan rahotannin ba su yi la’akari da ƙoƙarin da ake yi a ƙarƙashin tsarin majalisar zartarwa na amfani da naira wajen sayar da ɗanyen mai da man fetur a cikin gida da ba,” in ji sanarwar.
“Kawo yanzu ba a ɗauki wani mataki na daina wannan tsarin ba kuma ba a tunanin yin hakan,” in ji Adedeji.
Ya ƙara da cewa bayan an ɗabbaka tsarin na watanni, alamu sun nuna cewa tsarin ne hanya mafi dacewa a bi kuma zai ci gaba da taimaka wa tattalin arziƙin ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa tsarin na sayar da ɗanyen mai a cikin gida an tsara shi ne domin inganta yanayi na gasa da inganci na farashi.
“Mun duƙufa wajen tabbatar da aiwatar da wannan tsarin bisa manufofinta na inganta tace mai a cikin gida da rage amfani da kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma daidaita samar da mai a cikin gida,” in ji sanarwar.