NIJERIYA
2 minti karatu
An kama mutum huɗu da ake zargin 'yan bindiga ne a Kano
Rundunar 'yan sandan Nijeriya reshen Kano ta ce ta kama mutanen ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu game da mutanen kan cewa sun je Kano ne da niyyar sayen bindigar AK-47.
An kama mutum huɗu da ake zargin 'yan bindiga ne a Kano
SP Kiyawa ya bayyana cewa rundunar ta samu ci gaba sosai a yunƙurinta na daƙile kwararar ‘yan bindiga a jihar.
9 Maris 2025

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kano ta kama mutum huɗu waɗanda ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da lamarin a ranar Asabar inda ya ce sun kama mutanen ne bayan bayanan sirrin da suka samu game da su kan cewa sun je Kano ne da niyyar sayen bindigar AK-47.

Ya bayyana cewa zuwa yanzu, rundunar ta samu ci gaba sosai a yunƙurinta na daƙile kwararar ‘yan bindiga a jihar.

Ya bayyana cewa “A ranar 6 ga Maris ɗin 2025, da misalin 2:00 na rana, tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin SP Ahmad Abdullahi, jami’in da ke kula da ofishin Jar Kuka da ke Kano, ta kama mutum huɗu da ake zargi ‘yan bindiga ne a gidan mai na Chula da ke Hotoro Kwatas a Kano.

“Waɗanda ake zargin sun haɗa da Shukurana Salihu mai shekara 25 da Rabi’u Dahiru mai shekara 35 da Ya’u Idris mai shekara 30 duka daga Katsina sai kuma Mukhtar Sani mai shekara 30 daga Yandodo Hotoro Kwatas a Kano, kuma an kamasu sakamakon bayanan sirrin da aka samu cewa shun shigo Kano domin su sayi bindigar AK-47,” in ji Kiyawa.

Bayan ‘yan sanda sun gudanar da bincike a kan mutanen, sun gano wasu abubuwa a tattare da su waɗanda suka haɗa da bindiga ƙirar pistol mai sarrafa kanta ƙirar gida guda uku, da harsasai 12 irin daban-daban.

Haka kuma akwai harsashen bindigar farauta huɗu da ƙanana boris 24 da wuƙaƙe huɗu da adda ɗaya da kuɗi naira miliyan ɗaya da dubu ashirin da takwas da ɗari takwas.

Haka kuma ‘yan sandan sun samu mutanen da wasu layu waɗanda ake zargin na tsafi ne.

‘Yan sandan sun ce yanzu haka ana gudanar da bincike a kan mutanen a sashen binciken manyan laifukka na rundunar ‘yan sandan Nijeriya a jihar.

 

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us