Jami'an tsaron Syria sun daƙile wani hari da ragowar masu goyon bayan gwamnatin Assad suka kai kan kamfanin man fetur na SADCOP da ke Latakia a arewa maso yammacin ƙasar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar SANA ya ruwaito cewa, wata majiyar tsaro ta tabbatar mata da cewa, wani ayarin motocin jami'an tsaron sun taso daga lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria inda suka nufi zuwa gabar teku domin fatattakar sauran masu biyayya ga gwamnatin Assad da kuma tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
Majiyar ta ce an daƙile harin da aka kai wa SADCOP, ba tare da bayar da karin bayani ba.
A cikin 'yan kwanakin nan, lardunan Latakia da Tartus da ke gabar teku sun gamu da tashe-tashen hankulan a daidai lokacin da masu biyayya ga Assad ke ci gaba da kai hare-hare.
Waɗannan hare-haren - wanda aka bayyana a matsayin mafi muni tun bayan kifar da gwamnatin Assad a cikin watan Disamba – sun rinƙa kai hari kan jami’an tsaro da ke aikin sintirin da shingayen bincike da asibitoci wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkatr wasu.
A martanin da jami'an tsaro da sojoji suka yi, sun ƙaddamar da samame domin zakulo maharan. Samamen da suka ƙaddamar ya jawo mummunar arangama inda jami’an gwamnatin ta Syria suka bayyana cewa abubuwa sun kusan lafawa.
Ƙalubalen da ake sa ran fuskanta
Shugaban kasar Syria Ahmed Alsharaa ya ce an shawo kan matsalolin tsaro na baya-bayan nan a yankin gabar tekun kasar, yana mai bayyana su a matsayin "kalubalan da ake tsammanin fuskanta."
"Rikicin ya wuce lafiya," in ji Alsharaa bayan halartar Sallar Asuba a wani masallaci da ke gundumar Al Mezzeh a birnin Damascus kamar yadda wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna.
“Abin da ke faruwa a kasar ƙalubale ne dama da aka yi tsammani. Dole ne mu lazimci hadin kan kasa da zaman lafiya a tsakanin Siriyawa," in ji shi.
Ya kara da cewa "Muna iya zama tare a kasar nan iya gwargwadon iko."