Hukumar Yaƙi da Cutar da ke karya garkuwar jiki ta Nijeriya (NACA) ta yi watsi da wani labari da ke yawo a kafofin sada zumunta na intanet game da janye tallafin magungunan rage kaifin cutar da take bayarwa kyauta.
Shugabar hukumar ta NACA, Dr Temitope Ilori ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Ilori ta ce babu ƙamshin gaskiya a labarin cewa daga yanzu za a riƙa sayar da kowane maganin ARV a kan farashin Naira 250,000, kana ana buƙatar mai ɗauke da ƙwayar cutar HIV ya biya Naira 500,000 a duk wata.
“Maganin cutar HIV a Nijeriya kyauta ne a dukkan cibiyoyin kiwon lafiya da gwamnati ta amince da su. Gwamnatin Amurka da USAID da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ba su janye tallafin kuɗi kan maganin cutar HIV a Nijeriya ba,” in ji ta.
Shugabar ta jaddada ƙudurin hukumar na tabbatar da samar da maganin cutar HIV a wadace ba tare da katsewa ba.
Ta ce haɗin gwiwa da hukumar take da shi da abokan hulɗarta da tallafinsu yana nan kuma za a ci gaba da samar da kuma bai wa duk mai buƙatar maganin cutar a kyauta.
Ta kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da jita-jita, tana mai ƙarawa da cewa aikin da hukumar NACA ta sa a gaba shi ne ci gaba da taƙaita cutar HIV a Nijeriya.
Shugabar ta kuma yi gargaɗin a guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihanci da kuma tantance su ba, tana mai cewa hakan na iya haifar da fargaba tare da janyo tsaiko a yaƙin da ƙasar take yi da cutar HIV/AIDS a ƙasar.