Rundunar sojin Nijeriya ta ceto wasu fararen-hula 75 da ‘yan kungiyar Boko Haram/ISWAP suka yi garkuwa da su a dajin Sambisa da ke jihar Borno a ranar Litinin.
Hakan ya biyo bayan wani samame da dakarun sojin suka kai na fatattakar ‘yan ta’addan, kamar yadda babban kwamandan runduna ta 7 a dakarun sojin ƙasar, Manjo Janar W. Shaibu ya shaida wa manema labarai.
Manjo Shaidu wanda ya wakilci mataimakin kwamandan rundunar Brig. Janar A.L. Akpodu ya ce, mutanen da aka ceto sun hada da manya maza bakwai da mata 34, da kananan yara 34.
A cewarsa, a farmakin da runduna ta musamman ta 21 da kuma bataliya ta 199 da ke karkashin Operation Desert Sanity IV suka aiwatar, sun yi nasarar tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan a muhimman wurare da suka hada da Ukuba, da Ujimla, da Sabil Huda, da Garin, Fajula, da kuma Gobara.
“A ci gaba da kokarin da muke yi na fatattaka da kuma kawar da ‘yan ta’adda, a kwanan nan dakarun runduna ta musamman ta 21 da kuma bataliya ta 199 sun yi nasarar kai farmaki dajin Sambisa,” inji shi.
"An kuma share maɓoyar 'yan ta'adda, hakan ya ba da damar ceto fararen-hula 75, " kamar yadda ya tabbatar.
Brig. Janar Akpodu ya kuma ƙara da cewa, samamen da aka kai yankin ya matuƙar rage karfin ‘yan taddan inda aka kawar tare da lalata wasu muhimman kayayyakinsu da suka hada da manya-manyan makamai da ababen fashewa da kuma sansanonin da suke bayar da umarnin ayyukansu da dai sauransu.
Tuni dai aka miƙa mutanen da aka ceto don duba lafiyarsu, kafin an shirya sada su da ‘yan’uwansu.