Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) na shirin tattaunawa a cikin kwanaki masu zuwa domin tunkarar ƙalubalen da 'yan Nijeriya ke fuskanta wajen neman biza, a cewar wata sanarwa da Ƙaramar Ministar harkokin wajen ƙasar Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta fitar a ranar Lahadi.
Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan hanyoyin warware matsalolin da ke tattare da takunkumin ba da izinin shiga UAE da kuma ƙarfafa hulɗar diflomasiya da tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
An cim ma wannan matsaya ne a yayin ziyarar da jakadan UAE a Nijeriya, Salem Saeed Alshamsi ya kai ofishin Ƙaramar Ministar kan batun da ya shafi matsalolin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta wajen samun bizar ƙasar UAE, musamman bizar yawon buɗe ido
Ƙaramar Ministar ta yi nuni da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya da kuma haɗin-gwiwa a fannin tattalin arziki da ke tsakanin Nijeriya da UAE bisa ga yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu.
Ta jadadda cewa Nijeriya ta ƙuduri aniyar raya wannan dangantaka da aka kwashe tsawon shekaru da dama ana yi.
‘’Dubai ta zama wurin da ‘yan Nijeriya da dama suka fi kai ziyara, akwai ‘yan Nijeriya kusan 12,000 da ke zaune a UAE’’ in ji Bianca.
A cewar Ƙaramar Ministan, a shekarar 2015, kusan 'yan Nijeriya miliyan ɗaya ne suka ziyarci Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda suka kashe tsakanin dala miliyan 100 zuwa dala miliyan 150 wajen biyan kuɗin biza kaɗai da kuma fiye da dala biliyan 1 wajen sayayya da yawon buɗe ido, da kuma sauran harkokin tattalin arziki.
A shekarar 2022 ne, UAE ta ƙaƙaba wa Nijeriya takunkumin hana shiga ƙasar saboda taƙaddamar diflomasiyya.