DUNIYA
2 minti karatu
An yi wa wata 'yar Isra'ila fyaɗen taron-dangi a Indiya
'Yan sanda a ƙasar Indiya sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin amma sun kama mutum biyu a cikin waɗanda ake zargi.
An yi wa wata 'yar Isra'ila fyaɗen taron-dangi a Indiya
Biyu daga cikinsu, har da wani ɗan Amurka sun tsira, inda ɗayan mutum kuma aka gano gawarsa a ranar Asabar da safe. / Reuters
9 Maris 2025

An kashe wani mutum sannan wasu maza uku sun yi wa wata ‘yar Isra’ila ‘yar yawon buɗe-ido da kuma wata ‘yar ƙasar Indiya fyaɗen taron-dangi a kusa da wani sanannen wurin tarihi a kudancin Indiya, kamar yadda ‘yan sandan ƙasar suka tabbatar a ranar Asabar.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mutumin ɗan Indiya da matan biyu ke kallon taurari tare da wasu maza biyu ‘yan yawon buɗe-ido a garin Hampi inda kwatsam wasu maza uku suka far musu bayan gardama kan kuɗi, kamar yadda wani ɗan sanda Ram Arasiddi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sai da maharan suka tura mazan cikin magudanar ruwa kafin su yi wa matan fyade, in ji shi.

Biyu daga cikinsu, har da wani ɗan Amurka sun tsira, inda ɗayan mutum kuma aka gano gawarsa a ranar Asabar da safe.

‘Yan sandan ƙasar sun kama biyu daga cikin waɗanda ake zargi da kai harin, inda yanzu haka ‘yan sandan ke ci gaba da bincike.

Hare-haren da aka kai wa mata a Indiya ya ɗauki hankulan duniya a bara, bayan da aka yi wa wata karamar likita fyade kuma aka kashe ta a wani asibiti da ke gabashin birnin Kolkata da ke gabashin kasar, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar da kuma zanga-zangar rashin tsaro ga mata.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us