Kocin Liverpool, Arne Slot ya amsa cewa yana shakkar wasan da za su buga da PSG a Gasar Zakarun Turai yau Talata.
Slot ya ce ba ya iya barci saboda wasan, wanda zai fayyace ƙungiyar da za ta wuca matakin na ‘yan-8 a gasar mai matuƙar muhimmanci.
Yayin da yake kiran PSG a matsayin ƙungiya mafi iya taku da ya fuskanta, kocin ya ce suna yin iya yinsu don ganin sun shirya wa wasan.
A makon jiya ne Liverpool ta je birnin Paris ta kara da PSG a zagayen farko na wasan mai hannu biyu, wanda ya ƙunshi ƙungiyoyi 16.
PSG ƙarƙashin Koci Luis Enrique, sun nuna ƙarfi a wasan, amma a ƙarshe Liverpool ta yi nasarar cin ƙwallo guda.
Wannan dalili ya sa kocin Liverpool ya bayyana yadda yake tararrabin karawarsu ta biyu da PSG, wadda za ta gudana a gidan Liverpool da ke Anfield, da maraicen Talatan nan.
Kasa barci
Manema labarai sun tambayi kocin ko yana mafarki mai kyau kan haɗuwarsu da PSG a Anfield.
Slot ya ce "A’a, ba za ka yi mafarki ba, dole ka yi aiki tuƙuru don shirya ƙungiyarka da kyau. Ina ƙoƙarin yin hakan kan wannan wasan”.
“Idan kana fuskantar [sake wasa da PSG] tamkar irin wanda muka yi makon jiya, za ka fara tunani ko za ma ka iya yin barci!”
“Ban yi mafarki ba wannan satin; muna mai da hankali, makon nan ya fara mana da kyau ranar Asabar, kuma yanzu muna fatan ganin gobe. Kowa na fatan zuwan wannan wasan."
Liverpool za ta yi fatan wasan na yau zai mata sauƙi saboda a tsakiyar masoyanta za ta yi, inda take fatan wucewa matakin kusa da na ƙarshe a gasar ta UEFA.