Daga Jolezya Adeyemo
Daya daga muhimman abubuwan da aka nuna su a gidan Adana Kayan Tarihi na Kasa da ke Lusaka a Zambia shi ne wani kokon kan Broken Hill Man
Wannan kokon kan na dan adam, an gano shi ne a 1921 a garin Kabwe, mai nisan tafiyar awanni uku daga Lusaka. An bayyana shi a matsayin “kokon kan dan adam na farko a tarihin dan adam da aka gano a Afirka”.
Sai dai kuma, an yi tuya an manta da albasa a wajen nuna kayayyakin. Abin da za ka gani a Lusaka ba shi ne ainihin kokon kai na ‘Broken Hill Man ba‘, an kwaikwaye shi ne kawai.
A 1921, Zambia na karkashin mulkin mallakar Birtaniya, kuma bayan an gano shi, an dauke kokon kan na Broken Hill Man zuwa Birtaniya tare da bayar da kyautarsa ga Gidan Adana Kayan Tarihi na Landan, inda har zuwa yau ana nuna shi ga maziyarta.
Kira ga yin adalci
A farkon 2023, na ziyarci Gidan Adana Kayan Tarihi na Kasa kuma dan jagorana ya tabbatar min da cewa kokon kai na Broken Hill Man, wanda aka fi sani da ‘Kabwe Man’, zai dawo Zambi a wannan shekarar.
Abin takaici, har yanzu ba a yi hakan ba. Tun 1972, gwamnatin Zambia ke ta gangami da kira kan a dawo mata da Broken Hill Man, amma hakan ya ci tura.
A martani ga sabbin kiraye-kirayen da gwamnatin Zambia da ‘yan kishin kasa ke yi, UNESCO ta yanke hukunci a 2024 inda ta umarci Birtaniya da ta mayar da kokon kan, amma har yanzu ta ki yin hakan.
Kokon kan Broken Hill Man daya ne daga kayan tarihi da al’adu masu yawa da aka dauka daga Zambia da wasu kasashen Afirka, wadanda a yanzu suke Gidajen Adana Kayan Tarihi na Turai.
Ba wai diban wadannan kayan tarihi kawai aka yi ba, kwace su aka yi ba tare da yarda ba a karkashin mulkin mallaka, aka yi watsi da muhimmancinsu ga al’ummun da aka kwacewa su. Yau, suna nan a a cibiyoyin da ake amfana da nuna wa jama’a su, inda aka hana asalin kasashen da suka fito mallakar kayansu na tarihi da nuna wa jama’arsu su- tare da ma haramta musu amfana da kudaden shigar da ake samu daga masu zuwa kallon su.
Akwai kimanin kayan tarihi mallakin Afirka guda 500,000 a cibiyoyin Turai da Amurka. A gidan Adana Kayan Tarihi na Musée royal de l’Afrique Centrale da aka sani da sunan Gidan Tarihin Afirka, kadai, za a samu guda 180,000.
Gidan Adana Kayan Tarihin ya samo asali ne tun lokacin Sarkin Belgium Leopold II, wanda da karfin zalunci ya mulki Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a matsayin yankinsa na mulkin mallaka na musamman, inda kimanin ‘yan Kongo miliyan 10 suka mutu a karkashin mulkinsa.
A shekarar 1897, ta karfi da yaji aka dibi maza da mata da yara kanana ‘yan kasar Kongo su 267 aka kai su Belgium, inda aka saka su a keji ana kallo don nuna karfin mulkin mallaka. , Wajen da aka nuna su ne ya zama Gidan Tarihin Afirka a yau. Wannan misali daya ne kawai daga cikin munanan ta’annatin da ke tattare da kayan tarihin Afirka.
Dawo da kayayyaki ta yanar gizo
A ‘yan shekarun nan, an samar da tsarin dawo da kayayyaki ta yanar gizo don jin an mallake su.
Misali, Gidan Adana Kayan Tarihi na Mata na Zambia ya fara adana kayan tarihin Zambia da ke Sweden ta hanyar yanar gizo. Goidan Adana Kayan Tarihin Rayuwar Jama’a na Sweden na dauke da kayan Zambia sama da 600. Manufar dawo da kayan ta yanar gizo ita ce ilmantarwa da bai wa jama’ar Zambia damar sani da fahimtar kayansu na tarihi.
Wadannan kayayyaki sun hada da kwandunan kamun kifi da takunkuman biki, da ma wasun su. A yayin da ake yaba wa wannan mataki da yadda ake samun ci gaba, ana bukatar daukar babban mataki. Ganin kayan tarihi ta yanar gizo na da amfani sosai amma fa ba zai taba maye gurbin a ce na asali ne ake gani ba, kuma hakan ba zai kawar da rashin adalcin da aka yi ba.