NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin sanƙarau fiye da kwalba miliyan ɗaya daga Cibiyar Gavi
Nijeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen da cutar ta fi ƙamari a Afirka, inda aƙalla mutum 1,700 suka kamu da cutar a shekarar da ta gabata kuma cutar ta kashe fiye da mutum 150 a jihohi bakwai.
Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin sanƙarau fiye da kwalba miliyan ɗaya daga Cibiyar Gavi
'Yan shekara 1 zuwa 29 da cutar ta fi shafa ne za a fara bai wa rigakafin na sanƙarau / AP
5 Afrilu 2025

Nijeriya ta karɓi allurar rigakafin sanƙarau fiye da kwalba miliyan ɗaya daga asusun yaƙi da cutar a ƙasa mafi yawan al’umma a Afirka tare da tallafin cibiyar samar da rigakafi ta GAVI  a ranar Juma’a.

Nijeriya ɗaya ce daga cikin ƙasashen da cutar ta fi ƙamari a Afirka, inda aƙalla mutum 1,700 suka kamu da cutar da shekarar da ta gabata, sannan ta kashe fiye da mutum 150 a jihohi bakwai.

Gavi, cibiya ta haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kamafanoni masu zaman kansu wadda ke taimaka wajen samar da kuɗade domin bai wa ƙasashe masu tasowa rigakafi, ta ce wannan allurar rigakafi ta farko za ta taimaka wajen yaƙar annobar sanƙarau da ta ɓarke inda za a bai wa mutane masu shekara 1 zuwa 29, waɗanda cutar ta fi shafa.

Za a ƙaddamar da yin rigakafin ne a jihohin Kebbi da Sokoto tare da shirye-shiryen faɗaɗa ba da rigakafin zuwa jihar Yobe idan aka samu ƙarin rigakafin, in ji Gavi

Nijeriya ta kasance ƙasa ta farko a duniya wadda ta fara bayar da nau’in rigakafin sanƙarau na Men5C a shekarar da ta gabata, in ji hukumar lafiya ta duniya (WHO).

An fi samun ɓullar cutar ne a lokacin rani, tsakanin watan Disamba zuwa watan Yuni, inda cutar ke kai ƙololuwa tsakanin watan Maris da watan Afrilu, lokacin da ake samun ƙarancin danshi da kuma yawan ƙura.

Sanƙarau cuta ce da ta shafi kunburin tsokar da ke kewaye da ƙwaƙwalwa da kuma ƙashin baya wadda yaɗuwar ƙwayoyin halitta ka iya janyowa. Cutar ta fi yaɗuwa ne ta hanyar sumbata da atishawa da tari da kuma zama kusa da mutane da yawa.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us