WASANNI
2 minti karatu
Christian Chukwu: Hukumar kwallon Nijeriya ta musanta cewa tsohon kocin ya rasu da bashinta
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, NFF ta musanta cewa tsohon kocin Super Eagles da ya rasu yana bin hukumar bashin kuɗaɗe.
Christian Chukwu: Hukumar kwallon Nijeriya ta musanta cewa tsohon kocin ya rasu da bashinta
Christian Chukwu ya mutu yana da shekara 74 a duniya / TRT Afrika Hausa
14 Afrilu 2025

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF ta musanta zargin da ake mata na cewa tsohon kocin tawagar ƙasar ta Super Eagles wanda ya rasu ranar Asabar 12 ga Afrilu, yana bin hukumar bashi.

NFF ta ƙalubalanci duk wani da ke da ƙwaƙƙwarar hujjar takardu da ke nuna cewa akwai wani tsohon koci da ke bin ta bashi cikin shekaru 20 baya, da ya bayyana tare da hujjojinsa.

Martanin hukumar na zuwa ne bayan maganganun da ake a shafukan sada zumunta suna iƙirarin cewa NFF ta riƙe kuɗaɗen kyaftin ɗin tawagar Nijeriya da ta lashe kofin Afirka a 1980, wanda ya ka dala $128,000.

Sakataren hukumar, Mohammed Sanusi ya ce, “Babu wata sheda da ke nuna NFF tana da bashin Christian Chukwu a kanta. Lokacin wa’adin mulkin Mr. Amaju Pinnick, an kafa kwamitin yin duba kan takardun koci-kocin da ke ake bi bashi, har da na shugabannin NFF na baya”.

“Ina sane da cewa '[Christian Chukwu] ya yi aiki da NFF tsakanin 2002 da 2005, kafin a sallame shi daga muƙami bayan canjaras 1-1 da Angola a wasannin cancantar buga Kofin Duniya na FIFA a Kano a Agustan 2005. Tabbas babu shaidar ana bin NFF bashi.”

Sakataren ya ƙara da cewa “A matsayinmu na hukuma mai kima da ke tsayuwa kan ayyukanta, idan aka gabatar mana da duk wasu ƙwararan takardu nuna wani koci na bin mu bashi, to za mu biya bashin nan-take.”

Tsohon kofin na Super Eagles da ake wa laƙabi da ‘Chairman’ saboda tashensa da kwarjininsa, ya rasu yana da shekaru 74 a ƙarshen makon jiya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us