TURKIYYA
3 minti karatu
Turkiyya na shirin gudanar da ayyuka fiye da 60 na Duniyar Wata a shekaru goma masu zuwa
Aikin Duniyar Wata na Turkiyya ya haɗa da bunƙasa fasaha don auna tururi da ɗauka hotunan Duniyar Wat da ma binciken kan asalin dandaryar ruwa ta watan.
Turkiyya na shirin gudanar da ayyuka fiye da 60 na Duniyar Wata a shekaru goma masu zuwa
Türkiye is preparing for its first lunar mission by 2028. / AP
10 Afrilu 2025

Turkiyya na shirin gudanar da ayyuka fiye da 60 na Duniyar Wata shekaru goma masu zuwa a ƙoƙarinta na samun dama mai girma ta taka rawa a binciken Duniyar Wata da ƙasashen duniya ke yi.

Shirin binciken Wata na ƙasar ya haɗa da ƙirƙirar kayayyakin fasaha na zamani don auna haske da tururi d daukar hotunan saman Wata, da binciken asalin ruwa a saman Wata.

Tattalin arzikin Duniya da Wata, wanda manyan masu ruwa da tsaki a binciken Wata ke jagoranta, ana sa ran zai kai darajar dala biliyan 150 nan da shekarar 2040, bisa ga bayanan da Anadolu ta tattara.

Shirye-shiryen da NASA ke jagoranta, ciki har da Gateway wani kamfani mai yin ayyukan binciken duniyar Watan da Artemis, suna aiki don kafa sansani na dindindin ga ɗan’adam a Duniyar Wata.

Waɗannan shirye-shiryen suna da burin mayar da Wata ya zama tashar cika tankunan jiragen sama-jannati da mai, ta amfani da albarkatun sararin samaniya don tallafa wa zurfin binciken sararin samaniya.

A ƙarƙashin Shirin Sararin Samaniya na Ƙasa, Turkiyya tana shirin gudanar da aikin binciken Wata na farko nan da shekarar 2028.

Ƙasar tana da burin zama jagora a binciken Wata ta hanyar isa ga tauraron duniya tare da jirgin da aka ƙera a ƙasar tare da tsarin tura jirgi na gida.

Shirin binciken Wata na Turkiyya ya haɗa da haɓaka fasahohi daban-daban, kamar na'urar hangen Wata da ta auna tururi da kyamarori masu girma da ɗaukar hoto tar-tar don bincike da daukar hotunan dandaryar Wata.

Manufar shirin ta haɗa da gano asalin ruwa a dandaryar Wata da nazarin tsarin maganaɗisu da binciken yanayi a Duniyar Wata, da kuma tantance matakan tururi duka a saman Wata da kuma a cikin sararin duniya.

Ta hanyar Shirin Sararin Samaniya na Ƙasa, Turkiyya tana matsayi don bayar da gudummawa ga tattalin arzikin sararin samaniya da na Wata wanda ke kara girma cikin sauri.

Akwai manyan fannoni uku da ke tsara tattalin arzikin Wata: sufuri zuwa Wata, tattara bayanai daga tauraron duniya, da tantance albarkatu. Türkiye na iya bayar da gudummawa ga waɗannan fannoni tare da ƙwarewarta da tsarin ta.

Samar da wannan burin ya haɗa da masana'antu da yawa fiye da na sararin samaniya kawai.

Masana'antu kamar na motoci da gine-gine da mutum-mutumo da sadarwa da haƙar ma'adanai da kiwon lafiya, da sufuri suna bayar da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin Duniyar Wata.

Tattalin arzikin Wata mai girma kullum

Kasuwar sufuri zuwa Wata ana sa ran za ta kai dala biliyan 79 nan da shekarar 2040.

Wannan ya haɗa da haɓaka tsarin harba jirage da sufuri a cikin sararin samaniya, da tsarin sauka a saman Wata, tare da tallafin ayyuka da sarrafa bayanan aikin.

Muhimman abubuwan wannan kasuwa sun haɗa da tauraron ɗan’adam da jiragen sauka da motocin bincike na sararin Wata da tsarin sauka da kewayawa da ayyukan sarrafa jirage da sadarwa da watsa bayanai, da sarrafa bayanan aikin.

Kasuwar samar da bayanai daga Wata, wadda ta haɗa da samarwa da sufuri da bincike daga nesa da na wurin da sarrafa bayanai kafin amfani da ajiya da kuma nazari, ana hasashen zai kai dala biliyan $8.3 nan da shekarar 2040.

Bugu da ƙari, bincike da haƙowa da sufuri da tacewa da samarwa, da kuma samar da albarkatun Wata an ƙiyasta zai kai girman kasuwa ta dala biliyan $64 nan da shekarar 2040.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us