Ademola Lookman, ɗan wasan Atalanta ɗan asalin Nijeriya zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar da yake buga Gasar Serie A ta Italiya.
Rahotanni na cewa zuwa yanzu an kawo ƙarshen taƙaddamar da aka yi fama da ita tsakanin Atalanta da Inter Milan, kan ƙoƙarin Lookman na sauya sheƙa zuwa can.
A yanzu, Lookman zai ci gaba da zama a Atalanta kuma zai koma halartar atisaye ‘yan wasan ƙungiyar da ya ƙauracewa a farkon kakar bana.
A makonnin da suka gabata, Lookman ya yi jiran rashin tabbas sakamakon haƙilon da ya yi na sauya sheƙa zuwa Inter.
A Agusta, dangantaka ta yi tsami tsakanin Ademola Lookman da Atalanta har ta kai ɗan wasan ya goge hotunansa na ƙungiyar daga shafukansa na soshiyal midiya.
Manta baya
Inter dai ta miƙa tayin dala miliyan 53 kan ɗan wasan amma sai Atalanta ta ƙi amsa, wanda a ƙarshe ya janyo cinikin ya rushe.
A halin yanzu bayan dawowarsa daga buga wa ƙasarsa Nijeriya wasa, Lookman ya koma tawagar da koci Ivan Juric ke jagoranta.
Atalanta dai ta dage wajen ƙin rabuwa da zaratan ‘yan wasanta na gaba, duk da tayin da ta samu daga Inter.
A kakar bara, Lookman ya ciyo wa Atalanta ƙwallaye 20 a duka gasanni.
Yanzu dai za a jira ganin yadda Ademola Lookman zai manta baya ya taya Atalanta yaƙin neman kofuna a kakar bana.