Tsohon ɗan wasan Tottenham ɗan asalin Argentina, Erik Lamela ya bayyana yadda ya kwashe shekaru 11 yana fama da ciwon kwankwaso, har ta kai shi ga ritaya a yanzu.
Lamela ya ce ya kwashe shekara biyar yana shan maganin rage raɗaɗi kullum, kafin a yanzu ciwon ya tilasta masa barin buga ƙwallon ƙafa kacokan.
Ciwon kwankwason nasa ya fara ne sanda yana da shekara 22 amma bayan shekaru 11, yanzu ya ajiye but yana da shekaru 33 a duniya.
A wata tattaunawar bankwana da ya yi mai cike da bayyana gaskiya, ya ce hukuncin yin ritayar ya zo ne saboda fama da ciwon da ya yi tsawon sama da shekaru goma.
Tabarbarewar ciwo
Ya ce ciwon ya fara ne da ɗan ƙaramin zogi lokacin yana shekaru 22, amma sai ya yi muni yana dawowa, sakamakon siɗewar guringuntsi da hauhawar cutar osteoarthritis.
Yana shekaru 25, an yi wa Lamela tiyata, wanda ya taimaka masa ci gaba da wasa. Amma sai ciwon ya ci gaba da dawowa.
Erik Lamela ya buga wasa a ƙungiyoyin River Plate, AS Roma, Sevilla, AEK Athens, da kuma Tottenham, a inda ya kwashe kaka takwas, amma jinya ta hana shi gaban hantsi.
Ya kuma buga wa tawagar ƙasarsa Argentina daga 2011 zuwa 2018.
A yanzu dai, Erik Lamela ya kama aikin horarwa a Sevilla, inda yake da kyakkyawar mu’amala da kocin ƙungiyar Matias Almeyda, tun sanda yana wasa acan.