Tsawon shekaru, ‘yar wasan tseren Olympics, Favour Ofili ta kasance tauraruwa a fagen wasannin motsa-jiki a Nijeriya.
Ofili tana da lambobin zinare guda shida a Gasar Zakarun Duniya, kuma taɓa kai wa wasan ƙarshe a gasar mata ta mita 200 a wasannin Olympics na Tokyo.
Ita ce kuma mai riƙe da kambin duniya na gasar mita 150, wanda ya ba ta fifikon da tasirin jan ragamar sabon zamani a fagen wasanni na Nijeriya.
Amma duk da nasarorin da ta samu, dangantakarta da Hukumar Wasanni ta Nijeriya (AFN) ta kasance cike da rashin cin moriyar damammaki.
A gasar Tokyo 2021, Ofili ta rasa samun damar fafatawa saboda matsalolin gudanarwa na hukumar.
Sannan shekaru huɗu bayan nan a Paris, an hana ta shiga gasar mita 100 bayan an kasa ganin sunanta a jerin 'yan gasar tsere.
Wannan kuskuren da binciken gwamnati ya tabbatar ya faru ne sakamakon "rashin kula" daga hukumar AFN.
Zaɓar Turkiyya
A daren 1 ga Satumba, Favour Ofili, mai shekaru 22, ta sanar da sauya ƙasarta daga Nijeriya zuwa Turkiyya.
“Kamar yadda wasu daga cikinku suka ji, na fara sabon babi na wakiltar Turkiyya… Bayan fuskantar babbar rashin kulawa daga AFN da NOC a wasannin Olympics biyu (Tokyo/Paris). Na yanke wannan shawarar,” in ji Ofili a shafinta na Instagram.
Sanarwarta ta tabbatar da jita-jitar da ta yadu tsawon watanni kan cewa ta sauya ƙasarta. Sai dai AFN ba ta ce komai ba kan sanarwar Ofili ba.
Dokokin Hukumar Wasanni ta Duniya (World Athletics) sun tanadi cewa dole ne 'yan wasa su jira tsawon shekaru uku bayan yin wasansu na ƙarshe ga wata ƙasa, kafin su sauya ƙasa, sai dai idan an samu wani yanayi na musamman.
Favour Ofili ta nuna shirin jure wannan lokacin jiran, ko da hakan na nufin za ta rasa damar shiga gasar zakarun duniya ta 2025 a Tokyo.
Ta ce, “Ko da yake hakan na nufin rasa gasar bana a Tokyo, wannan sauyin ya fito daga zuciyata… Ina matuƙar godiya da samun sabon gida a Turkiyya“.