Maroko ta kafa tarihi ranar Juma’a, inda ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta fara samun gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2026 da za a buga a Chile, Arewacin nahiyar Amurka. Ƙasar ta samu gurbin ne bayan ta lallasa Nijar da biyar da nema a Rabat.
Wannan nasarar ta tabbarar da zaman Maroko a saman teburin rukunin E, duk da cewa tana da sauran wasannin biyu da za ta buga.
Kunnen dokin da Tanzaniya ta buga da Jamhuriyar Kongo a Brazzaville da farkon ranar ne ya bai wa Maroko damar samun gurbin shiga gasar.
Nasarar shiga Gasar Cin Kofin Duniyar da Maroko ta yi ta zama abin koyi ga masu son shiga gasar daga nahiyar Afirka kuma sauran tawagogin za su yi ƙoƙarin yin koyi da ita inda Nijeriya za ta kara da Rwanda ranar Asabar.
Yayin da sauran wasu ƙasashe ke da damar iya shiga gasar, alamu na nuawa cewa zuwa gasar Cin Kofin Duniya a ƙasar Chile zai kasace wata tafiya mai jan hankali wadda ba za a iya hasashen yadda za ta kaya ba.