TURKIYYA
3 minti karatu
Babu ja da baya a dukkan matakan tabbatar da Turkiyya marar ta’adanci: Erdogan
Da zarar an cim ma manufar tabbatar da kasa da yanki marasa ta’addanci, za a bude sabon shafi ga kasar, in ji Shugaban Ƙasar Turkiyya.
Babu ja da baya a dukkan matakan tabbatar da Turkiyya marar ta’adanci: Erdogan
"Gwamnati na daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ‘yan kasa miliyan 86 na rayuwa cikin kwanciyar hankali da ." / AA
7 Agusta 2025

Babu kofar bayar da kai bori ya hau, ja da baya, sulhu ko wani yunkuri na sirri a matakin samar da Turkiyya marar ta’addanci, in Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wata wasika da ya aike ga iyalan shahidai da ‘yan mazan jiya.

Erdogan ya jaddada cewa, duk wani taku na kasar nan cike yake da jinin shahidai da kuma ‘yan mazan jiya, yana mai cewa zaman lafiya, tsaro, da alfahari da Turkiyya ke samu a yau, sun samu ne saboda sadaukarwar da suka yi, kuma kare abin da suka bari shi ne babban aikin gwamnati.

"Ina roko da kuma kira gare ku da ku tabbata cewa babu wata kofa ta ja da baya ko bayar da kao bori ya hauc, tattaunawa, sasantawa da wani sirri a kowane lokaci a cikin wannan tsari, kuma ba za a samu damar yin hakan nan gaba ba."

Ya kara da cewa "Babu wani mataki da aka dauka, kuma ba za a dauka ba, wanda zai azabtar da rayukan shahidanmu masu daraja ko cutar da iyalan shahidanmu da kuma tsaffin sojojinmu."

Da zarar an cimma manufofin kasa da ba ta da ta'addanci, za a bude wani sabon babi ga kasar, in ji Erdogan, yana mai karawa da cewa: “'Yan uwantakarmu da ta shafe shekaru dubu za ta kai wani sabon mataki, kuma za a tumbuke tsagwaron sabani da aka shuka a tsakaninmu, kuma za a watsar da shi har abada.”

Erdogan ya kuma aike da wasika ga dukkan 'yan kasar kan manufar tabbatar da kasar Turkiyya da ba ta da ta'addanci.

Ya ce, suna ci gaba da yin aiki tukuru don samar da wata kasa mai karfi da girma ta Turkiyya, tare da sanin cewa suna daukar nauyin kowane dan kasa a wuyayensu.

‘Daukar aniyar kawo karshen zubar da jini’

Ya ce a cikin shekaru 23 da suka gabata, ta hanyar zuba jari da aka yi, da ayyuka, sauye-sauye, ayyuka da dokokin da aka aiwatar, an daukaka Turkiyya zuwa matsayi mai daraja a yankinta da kuma a matakin kasa da kasa.

Erdogan ya jaddada cewa, duk da irin kalubalen da aka sanya a gabansu, sun hada karfi da karfe da al'ummar kasar wajen karfafa dimokuradiyya, da fadada hakkoki da 'yanci, da kawar da tsarin danniya, da tabbatar da 'yancin kai na kasa a dukkanin cibiyoyin gwamnati.

Ya ce yayin da suke yakar duk wani nau’in ta’addanci ba tare da kakkautawa ba, suna daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ‘yan kasa miliyan 86 na rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa da ‘yan uwantaka.

“Tare da al’ummarmu, mun kudiri aniyar ruguza tushen zubar da jini da ya hana kasarmu cim ma muradunta na tsawon rabin karni, in Allah ya yarda a karshe za mu kai ga cim ma burin kafa Turkiyya da babu ta’addanci da kuma yankin da ba shi da ta’addanci,” inji shi.

"Na tabbata, mun san ainihin abin da muke yi kuma muna yin aiki tare da dabarun bayanan sirri, kulawa sosai, da aiki da hankali. Duk matakin da muka dauka ana lissafta shi ta hanyar tsanaki," in ji shugaban.

Ya kara da cewa, "A kokarinmu na samar da Turkiyya mara ta’addanci babu wani mataki da ba ni in ba ka, babu wata tattaunawa ko ja da baya, ko wani mataki da zai lalata ‘yancin makomarmu, kuma ba za a taba samun hakan ba,” in ji shi.

"Ba mu taba yarda ba, kuma ba za mu taba yarda da, duk wani yunkurin da zai cutar da rayukan shahidanmu masu daraja, ko ya bata wa sojojinmu rai, ko bakin ciki da kunyata iyalan jaruman da suka riga mu gidan gaskiya."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us